Shagon gyaran gashin masu sa hijabi
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An bude shagon gyaran gashin masu hijabi a Amurka

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

An kafa wani shagon gyaran gashi a birnin New York musamman domin wadanda ba su son maza su dinga ganin gashin su.

Masu aiki a shagon suna rufe gashinsu sannan kuma yawancin abokan cinikayyarsu ma suna rufe gashinsu.

Masu zuwa shagon suna jin dadin zuwa wannan shagon sosai saboda suna samu a kula da su ba tare da damuwa ko namiji zai gan su ba.

Yanzu matan za su iya zuwa su wala ba tare da wata fargaba ba.

Karanta wasu karin labarai

Labarai masu alaka