Kyautar Golden Boot: Salah da Mane da Aubameyang sun yi zarra

Mohammed Salah da Sadio Mane da Pierre-Emerick Aubameyang
Image caption Mohammed Salah da Sadio Mane da Pierre-Emerick Aubameyang sun jagoranci kungiyoyinsu ga nasarori daban-daban

Sadio Mane da Pierre-Emerick Aubameyang sun ci kwallaye a wasan karshe na Premier League domin su raba kyautar takalmin gwal ta dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a tsakaninsu.

Aubameyang ya ci wa Arsenal kwallo biyu a Burnley, wanda hakan ke nufin ya kamo Salah da abokin wasansa Mane a matsayin wadanda suka fi kowa zura kwallaye a gasar Peremier bana da aka kammala Lahadi.

Kowannensu yana da kwallo 22. Mane ya ci kwallo ta 21 da 22 a wasan karshe da Liverpool ta ci Wolves 2-0.

Salah ne ya ci kyautar a kakar da ta gabata.

Wannan ne karo na farko da sama da mutum biyu suka lashe kyautar tun bayan Dimitar Berbatov da Carlos Tevez da suka lashe Golden Boot din a shekarar 2010-2011 da kwallo 20 kowannensu.

Dan wasan Gabon Aubameyang, wanda ya ci kwallo biyu shi ma a filin wasa na Turf Moor ya ce: "Mun raba wannan kambu da 'yan wasa biyu da suke burge ni, zakakuran 'yan wasan Afirka. Mu wakilan Afirka ne. Abin ya yi dadi.

"Na ji dadi mun yi nasara. Abokan wasana suna sane da kyautar amma ban ce masu komai ba saboda ba na so su dogara da ni kadai. Gara mu yi aiki tare."

Image caption An bai wa Salah da Mane kyautar a lokaci guda

''Yan wasana ne baki dayansu'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An bai wa Aubameyang kyautar a Emirate bayan an tashi daga wasan da ya zura kwallo biyu a ragar Burnley

Kocin Liverpool ya nuna jin dadinsa ga tsohon dan wasaan Dortmund Aubameyang, wanda ya sayo shi a 2013 daga Saint-Etienne lokacin yana kocin Westfalenstadion.

"Har da Aubameyang ma? Duka sun yi nasara? Ya yi kyau. Dukkaninsu 'yan wasana ne," in ji Klopp

Salah mai shekara 26 ya ci kwallo 32 a kakar bara. Ya kafa tarihi, domin shi ne dan wasan da ya fara cin kwallo 32 a wasa 38.

Shi ne kuma dan wasa na shida da ya lashe kyautar a kaka biyu a jere.

Harry Kane na Tottenham da ya lashe kyautar sau biyu a jere - 2015-2016 da 2016-2017, ya kare kakar bana da kwallo 17, kakar da ya sha fama da rauni.