An dakatar da tattaunawar mika mulki a Sudan

Sudan
Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar sun ki cire shingayen da suka kafa a hedikwatar soji a Khartoum

Jagoran gwamnatin soji da ke mulkin Sudan ya ce an dakatar da tattauwar da ake yi da Jagororin da ke son tabbatar da mulkin dimokradiyya a kasar ta tsawon sa'oi 72.

Da ya ke jawabi ta gidan talbijin din kasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya ce za a kawar da shingayen da masu zanga-zanga suka sanya akan tituna a khartoum nan bada jimawa ba.

Wannan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan bangarorin biyu sun amince da kafa gwamnatin hadaka da mika mulki ga farar hula.

A jiya laraba an yi ta jin karar harbe-harbe da aka yi amanna sojoji ne ke yi dan firgita masu zanga-zanga su cire shingayen da suka kafa a hedikwatarsu da ke birnin Khartoum.

Masu zanga-zangar dai sun ce akalla mutane 9 aka ji wa rauni, sai dai kawo yanzu babu wani sahihin adadi.

Tashin hankali irin wannan da ya barke a ranar litinin ya yi sanadin mutuwar masu bore 6, inda suka kafe dole a hukunta sojojin da suka yi harbin.