Alabama: Za a daure likitan da ya zub da ciki shekara 90

Alabama
Image caption Mata da 'yan mata sun cika titunan jihar Alabama dan nuna adawa da dokar

Gwamnan jihar Alabama a Amurka ya rattaba hannu kan dokar hana zub da ciki kan kusan kowane yanayi, ciki har da fyade a wani mataki mai cike da ce-ce-ku-ce tun bayan hukuncin da kotun koli ta yanke da ya bai wa mata damar zubar da cikin.

Masu rajin kare hakkin jama'a sun sha alwashin zuwa kotu don hana amfani da dokar a Alabama, wadda tuni ta tunzura mata.

Kin san batun ya dade ya na janyo zazzafar muhawara a Amurka, inda masu rajin kare hakkin jama'a da na mata suke ta gudanar da zanga-zangar kin amincewa da dokar.

Ko a ranar Laraba da shi gwamnan Alabama ya rattaba hannu kan dokar an yi zanga-zanga.

Sai dai dokar ta ba da damar zubar da cikin idan rayuwar mahaifiya na cikin hadari.

Amma ta kara haramta zubarwa idan mace ta samu ciki sanadin fyade, wanda shi ne abun da ya fi dagawa masu rajin kare hakkin mata hankali.

Sannan wasu na ganin hakan zai sanya a samu likitocin bogi da wadanda ba su kware ba a wannan fannin.

Wata lauya mai rajin kare hakkin mata Gloria Allred ta shaida wa BBC cewa matakin zai cutar da mata, kuma lokaci ne mai cike da hadari ga mata da 'yan matan Amurka.

Ms Gloria ta kara da cewa dokar za ta hana likitoci zubar da ciki ko da kuwa a likitance ya dace a yi hakan, saboda idan har aka same shi da aikata hakan za a iya yanke masa daurin sama da shekara 90 a gidan kaso.

A karshe ta ce babbar matsalar ita ce matan da suke son zubar da ciki za su fara zuwa wajen likitocin da gwamnati ba ta san da su ba, wadanda ba su da lasi.

Babban hadarin shi ne, wasu za su iya rasa rayukansu kuma babu damar iyaye ko 'yan uwa su shigar da kara kotu tun da sun aikata abin da hukumomi suka haramta.

Labarai masu alaka