Kamfanin Huawei na tsaka mai wuya

Huawei
Image caption Huawei ne kamfani na biyu mafi girma da ke samar da wayoyin salula a duniya

Kamfanin laturoni na Japan wato Panasonic ya sanar da janye huldar kasuwanci da babban kamfanin wayar salula na Huawei tare da abokan huldarsa 86 don goyon baya ga matakin da Amurka ta dauka kan sa.

Panasonic ya kara da bayyana dakatar da dakon kayan babban kamfanin sadarwar na kasar China.

Harwayau haramcin da Amurka ta sanya ya hada da kashi 25 cikin 100 ko sama da haka na kayayyakin da Huawei ke samarwar ciki har da na kimiyya da dangoginsu.

A makon da ya wuce ma'aikatar kasuwancin Amurka ta dakatar da huldar kasuwanci da haramta wa kamfanin sayan kayan kasar bisa dalilan da suka shafi tsaron kasa.

Tsamin dangantaka da rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China a dan tsakanin nan, na daga cikin dalilan da wasu ke alakantawa da takunkumi da kauracewar da wasu kamfanoni ke yi daga Huawei.

A baya-bayan nan an sanya wa kamfanin takunkumin rashin samun damar amfani da manhajar Android zai shafi sabbin wayoyin kamfanin.

Karanta karin wasu labaran

Labarai masu alaka