Kalaman Buhari 'ba su dace da ministocinsa ba'

Ministocin Buhari Hakkin mallakar hoto Facebook/Nigerian Presidency

Jawabin Shugaba Buhari a taron majalisar ministocinsa ya janyo ce-ce-ku-ce, bayan yabawa da aikin ministocin tare da kin sauke su kafin cikar wa'adinsa na farko.

A ranar Laraba ne majalisar Ministocin ta Najeriya ta yi zamanta na bankwana kafin karewar wa'adin farko na mulkin Shugaba Buhari.

A yayin da yake jawabi, Shugaba Buhari ya ce irin rawar da ministocin suka taka ne dalilin da ya sa ya ci gaba da tafiya da su har tsawon shekara uku da rabi wato zuwa karshen wa'adinsa ba tare da ya sauya su ba.

Ya kuma ce ministocin za su ci gaba da rike ma'aikatunsu har sai nan da kwana bakwai masu zuwa lokacin da wa'adinsa na farko zai kare.

Sai dai kuma wasu na ganin jawabin na shugaban ya nuna alamun zai iya ci gaba da aiki da yawancin ministocin da suke ganin ba rawar da suka taka, kuma babu tabbas ko zai yi sabon zubi.

Dakta Abubakar Kari, mai sharhi kan lamuran yau da kullum a Najeriya ya shaida wa BBC cewa "babu tabbas ko shugaban zai bar wasu ko ma ya bar da dama daga cikinsu."

"Idan har kana tare da mutum kuma ka dinga yaba shi, to ba mamaki ci gaba da tafiya da shi kake son yi," in ji Kari

Ya kara da cewa tun tuni ya kamata a ce shugaban ya canza ministocinsa saboda "ba wata rawa da suka taka ko ci gaba da suka kawo ga ci gaban kasa."

Dakta Kari ya bayyana cewa akwai ministoci da dama da ba su taka rawar gani ba, kuma idan har shugaban zai ci gaba da aiki da wasu ministocin, "to ba su cancanta ba."

"Idan ka yi maganar ma'aikatu kamar na lafiya da sadarwa da na jiragen sama, ayyukan da ministocin suka yi bai gamsar da 'yan Najeriya ba."

"Sun kuma yi alkawura da dama kamar na magance matsalar wuta da kuma hanyoyi da suka kasa aiwatarwa," a cewarsa.

Dakta Kari ya jaddada cewa wadannan abubuwan da ya lissafo, ba wai yana nufin cewa ba su tabuka komai ba, "mutane dai ba su ga ayyukan da suka yi tunanin za a yi ba."

Wannan dai ba shi ne karo na farko da gwamnati take bai wa ministoci damar ci gaba da aiki har lokacin da aka rantar da sabuwar gwamnati ba.

Har yanzu babu wani takamaiman jawabi ko bayani da ya nuna cewa tabbas zai kara tafiya da su, ko kuma a'a.

A cikin jawabinsa ga ministocin, Buhari ya yi ikirarin cewa sun samu nasarar cika alkawuran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe, kuma ministocin sun taka rawa ga samun nasarar.

Masana harkokin tsaro da dama irinsu Malam Kabiru Adamu sun amince cewa shugaban ya samu gagarumar nasara a fannin tsaro - musamman a yaki da kungiyar Boko Haram wacce ta kashe dubban mutane sannan ta raba miliyoyi daga gidajensu.

Sai dai sun nuna gazawar shugaban wajen shawo kan matsalolin 'yan bindiga da masu satar mutane don karbar kudin fansa a jihohin arewa maso yammaci, matsalolin da suka yi kamari a yanzu.

Labarai masu alaka