Za a sabunta filin jirgin dakon kaya a Yobe

Gaidam
Image caption Fannin ilimi da kiwon lafiya na fama da matsala a jihar ta Yobe

Gwamnatin jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya ta yi karin bayani kan kudi sama da Naira Billiyan shida da ta amince da kashewa domin gyaran filin jirage saman dakon kaya da ke babban birnin.

Majalisar zartarwar jihar ce ta amince da kashe kudaden ranar Laraba ana kasa da mako daya kafin karewar wa'adin gwamnatin.

Jihar dai na daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro sakamakon tayar da kayar baya na Boko Haram, ga kuma kalubale ta fuskar kiwon lafiya da ilmi.

Wasu na ganin cewa bai kamata gwamnatin da wa'adin ta ke gab da karewa ta fara batun kashe makudan kudaden dan gudanar da aikin filin jirgin saman ba.

Akwai masu ra'ayin ko dai wata kafar ungulu ce, ake son yi wa asusun ajiyar gwamnatin ta yadda idan sabuwar gwamnati ta hau ba za ta samu ko sisi a asusun ba.

Amma mai magana da yawun gwamnan jihar Yobe, Abdullahi Bego ya musanta haka. Tare da shan alwashin jihar na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da za a samu asusunta a cike da kudi bayan mika mulki ga sabuwar gwamnati.

Labarai masu alaka