Na san manyan Najeriya ba sa kaunata – Buhari

Shugaba Buhari zai sha rantsuwa karo na biyu
Image caption Buhari ya ce zai sauya salo a karo na biyu

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce bai damu da rashin kaunar da manyan kasar suke nuna masa ba.

A wata hira ta musamman da gidan talabijin din kasar (NTA), Shugaba Buhari ya ce shi yana da yakinin cewa babu wani a kasar da zai iya samun kuri'un da ya samu a zabensa na farko da na biyu.

Ya ce yana da masaniyar cewa manyan kasar kwata-kwata ba sa kaunarsa, inda ya ce hakan ba ya damun sa ko kadan.

Da aka tambayi shi kan kamun ludayinsa dangane da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa a sabuwar gwamnatinsa da za ta fara ranar 29 ga wannan watan, sai Buhari ya ce "Zan kara wa 'yan sanda da kotu karfi" yadda ba za su tausaya wa masu laifi ba.

  • Latsa hoton da ke sama don kallon cikakkiyar tattaunawar.

Buhari ya sha alwashin cewa duk masu yi masa kallon yana 'tafiyar hawainiya' to za su kunyata domin za a ga wani Buhari ne daban.

Shugaba Buhari ya kuma dora alhakin lalacewar jami'an tsaro musamman sojoji ga shugabannin da suka yi mulki daga shekarar 1999 zuwa 2015, inda ya ce a lokacin ne aka samu tabarbarewar aikin da kuma rashawa da cin hanci.

Sai dai Buhari ya yaba wa masu rike da mukaman jagorancin sha'anin tsaro, inda har ya nuna cewa gwamnatinsa ta yi nasarar karya kungiyar Boko Haram.

Batu kan ministoci

Shugaban ya ce ba a taba samun wani ministansa ba da hannu a wata babbar badakala saboda haka yana da 'yancin da zai iya ci gaba da tafiya da duk ministan da ya so ya yi aiki tare.

Ya nemi 'yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu dangane da batun zaben ministocin da zai yi aiki da su saboda ba zai ba su kunya ba.

Sharhi daga Usman Minjibir

Akwai masu bayyana fargabar cewa Shugaba Buhari ka iya ci gaba da tafiya da ministocinsa a sabuwar gwamnati kasancewar shugaban ya furta da bakinsa cewa "ba a taba samun ministansa da wata babbar badakalar a zo a gani ba".

Sai dai kuma batun samun tsohuwar ministar kudin kasar, Kemi Adeosun da laifin mallakar shaidar kammala hidimar kasa ta jabu, al'amarin da ya janyo kiraye-kiraye daga kungiyoyi masu rajin yaki da almundahana na neman a sauke ministar.

Duk da an kai ruwa rana kafin gwamnatin Shugaba Buhari ta aiwatar da hakan, daga bisani ministar ta ajiye aikinta.

To sai dai watakila fadin da Buhari ya yi cewa "ba a samu ministansa guda daya da babbar almundahana ba", na nufin ministocin da yake tare da su a yanzu haka.

Tuni dai Shugaba Buhari ya umarci ministocinsa da su mika takardun ajiye aiki a ranar 28 ga watan nan wato kwana daya kafin rantsuwar sake kama aiki karo na biyu.

Labarai masu alaka