Iran ta mayar wa da Saudiyya martani

Hassan Rouhani
Image caption Dangantaka tsakanin Iran da Saudiyya ta kara tsami a dan tsakanin nan

Kasar Iran ta yi watsi da abin da ta kira zargin da bashi da tushe bare makama da aka yi mata a taron koli na kasashen yankin gabas ta tsakiya da ke gudana a kasar Saudiyya.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce Saudiyya ta hada kai da kasashen Amurka da Isra'ila da nufin ganin bayan ta.

Tun da fari sarki Salman bin Abdul'azeez al-Sa'oud ,ya yi kira ga kasashen da su mara masa baya don kawo abin da ya kira karshen taimakon da Iran ke bai wa kungiyoyin 'yan ta'adda da tsoma baki a harkokin kasashe.

Ya kuma kara da zargin Iran da kai wa jiragen dakon Mai na kasar Hari a Oman, zargin da Tehran din ta musanta.

Yawancin kasashen yankin Gulf sun rattaba hannun mara wa Saudiyya baya, ya yin da makwabciyar Iran kuma aminiyarta Iraq ta ki amincewa da hakan tare da cewa bai kamata a karya tsaron kasar ba.

Labarai masu alaka