Ka san dalilin da ya sa Musulmin Ghana ke sallah yau?

A bana ba bu bikin sallah a birnin Accra
Image caption Jawaban bikin sallar Idi a Ghana

A ranar Larabar nan ne al'ummar musulmin birnin Accra na kasar Ghana suka gudanar da sallar Idi a dandalin Black Star Square karkashin jagorancin limamin limamai na Ghana, Dr Usman Nuhu Sharubutu.

Musulman Ghana dai sukan dauki azumi su kuma sauke tare da sauran al'ummar musulmi na duniya, amma ba sa yin sallah tare har sai washe gari.

A wani jawabinsa, Limamin limaman na Ghana, Dr Usman Nuhu Sharubutu, ya ce "Litinin 3, ga watan Yuni ce rana ta karshe ta azumin watan Ramadan na shekara 1440."

Sai dai kamar yadda aka saba a kasar Ghana an dauki rana daya a matsayin ranar jajibiri kafin a gudanar da sallar idi.

Mafi yawan Musulmai a fadin duniya dai sun tashi da azumin watan Ramadan ranar shida ga watan Mayun 2019 inda aka kamala ran 3 ga watan Yunin 2019.

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa wasu al`ummar musulmi a Ghana sun gudanar da sallar idi tun ranar Litinin .

Hausawan Accra za su yi sallah lami

Image caption Masarautar Accra ba za ta yi bikin sallah ba

Da alama a karon farko Hausawan birnin Accra na Ghana za su yi karamar sallah lami ba tare da bukukuwan da ake yi a ranar ba.

Tuni dai shugabannin Hausawa a birnin suka bayar da sanarwar dage wadannan bukukuwa sakamakon karo da suka yi da wani bikin shuka da 'yan kabilar Ankarawa da ke birnin suke yi a duk shekara.

Hakan ne ya sa masarautar Hausawa ta birnin Accra sanar da cewar, za ta jinkirta hawan karamar sallah saboda bin umarnin dokar da masarautar Ankarawa ta kafa.

To sai dai wasu Hausawa mazauna Accra din sun ce ba su ga dalilin da zai sa a dakatar da bukukuwan sallah ba saboda wani biki.

A cewarsu hakan na nuni da irin rashin karar da 'yan kabilar ta Akarawa suka nuna wa Hausawa da musulmi.

Sai dai wasu na ganin dakatar da bukukuwan sallar da masarautar Hausawan Accra ta yi ya yi dai-dai saboda mutunta al'adar kabilun da suke zaune da su.

Labarai masu alaka