Tanzania ta haramta amfani da Leda

Tanzania
Image caption Tarar dala 90 ko zaman kaso na mako guda zai hau kan wanda ya take dokar

Tanzania da zamo kasa ta talatin da hudu a nahiyar Afurka da ta haramta amfani da leda a duk fadin kasar.

Duk wanda aka samu da saidawa ko amfani da leda ko nade kaya a kasuwa ko manyan shaguna za a ci shi tarar $90 kwatankwacin N 32,400 ko kuma daurin mako guda a gidan kaso.

Su kuwa kamfanonin da ke samar da leda za a ci su tarar dubban daloli da daurin kusan shekara biyu a gidan kaso.

Haramcin ya shafi matafiya da ke shiga kasar inda su ma tun a filin saukar jiragen sama da tasoshin mota za a umarci su mikawa jami'an da aka ware na musaman dan bincikar kayansu ciki har da jakar hannu ta mata.

Wannan matakin da Tanzania ta dauka da tarar da ta sanya mai sauki ce idan aka kwatanta da tsattsauran hukuncin da makofciyarta wato Kenya ta ke dauka kan wanda ya tade dokar.

Jami'an kula da muhalli na MDD sun ce yawancin kasashen da suka dauki matakin sun gagara samar da jakunkunan kwali ko na yadi da 'yan kasar za su yi amfani da su hakan na sanya jama'a cikin matsi.

Labarai masu alaka