Musulmin kasar Mali sun yi sallar Idi ranar Litinin

'Yan Najeriya na shirin yin sallah a ranar Talata
Image caption Watakila ranar Talata za a yi sallah a Najeriya

Da safiyar Litinin din nan ne al'ummar musulmi a kasar Mali suka yi sallar Idi karama bayan tabbacin ganin watan Shawwal da yammacin Lahadi.

Hakan na nufin Litinin din ta zama daya ga watan Shawwal ke nan a kasar.

Wata sanarwa da ministan harkokin addinin kasar ya sa wa hannu ya kuma aika ga kafofin sadarwar kasar ta ce " Gwamnati ta tsaida ranar Litinin 3 ga watan Yuni a matsayin ranar karamar Sallah ko El Fitr a fadin kasar Mali."

Sanarwar ta Ambato ministan na cewa an ga watan a wasu wurare na wasu yankunan kasar, kamar Kati da kuma Bamako fadar gwamnatin kasar.

Dan haka sanarwar ta ce ya zamo wajibi a yi sallah ranar ta Litinin a fadin kasar baki daya.

Al'ummar kasar ta Mali dai sun fara azumin watan Ramadan din ne ranar Lahadi ta hudu ga watan Mayu sabanin yadda akasarin kasashen musulmi a fadin duniya suka tashi da azumin ranar Litinin.

An ga wata a Zaria ta Najeriya

Mabiya mazhabar Shi'a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Elzakzaky sun ce yau daya ga watan Shawwal bayan samun tabbacin ganin wata da yammacin Lahadi.

Wata sanarwa da ke yawo a kafafen sada zumunta wadda kuma BBC ta tabbatar da sahihancinta ta sanar da mabiya mazhabar ta Shi'a dangane da ganin jaririn watan.

Sanarwar mai dauke da sa hannun malam Abdulhamid Bello daya daga cikin jagororin kungiyar 'yan uwa musulmi ta Islamic Movement of Nigeria, IMN, ta ce "Alhamdullah Yau lahadi (2/6/2019) mun samu wadanda suka tabbatar mana sun ga tsayuwar watan Shawwal a garin Dambo na Zaria da Lafiya na Jihar Nasarawa wanda hakan ya kawo mu karshen watan Ramadan."

Sanarwar ta kara da cewa " Ga wadanda suka fara azumi ranar litinin (6/5/2019) a bisa dogaro da rashin ganin wata za su rama azumi daya."

To sai dai sanarwar ta nemi mabiya da su yi sallah ranar Talata tare da sauran jama'a domin hadin kan musulmi.

"Batun taron idi ko kuma shagulgulan sallah, a yi la'akari da maslahar zamantakewar al'umma tunda yin su ba wajibi ba ne." In ji sanarwar.

Labarai masu alaka