An hana masu zanga-zanga fitowa a Kamaru

Maurice Kamto Hakkin mallakar hoto AFP

Babbar jam'iyyar adawa a Jamhuriyar Kamaru ta ce jami'an tsaro sun hana masu bore yin zanga-zanga a birnin Yaounde a ranar Asabar.

Jam'iyyar MRC dai ta shirya zanga-zangar matsa wa gwamnati lamba ta saki jagoranta Maurice Kamto da ake tsare da shi.

A watan Fabrairu ne aka gurfanar da shi gaban kotun sojin kasar kan zargin kitsa bore da yi wa gwamnati zagon kasa, kuma tun daga lokacin ne ake tsare da shi tare da wasu gwamman magoya bayansa.

An dai tsaurara matakan tsaron ne domin dakile zanga-zangar inda jami'an tsaro suka shirya tsaf domin watsawa masu zanga-zangar ruwan zafi.

To sai dai kuma magoya bayan jam'iyyar ta MRC sun sha alawashin cewa ba gudu ba ja da baya sai sun yi abin da suka yi niyya duk da jami'an tsaron da aka girke.

Wannan dai na zuwa ne bayan jam'iyyar MRC ta yi ta bore bayan zaben shugaban kasa a watan Oktoban bara wanda 'yan adawar suka ce an tafka magudi da aringizon kuri'u a zaben shugaban kasar da aka yi inda aka ayyana shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya samu nasara.

Labarai masu alaka

Karin bayani