Ko katse Intanet zai hana satar jarabawa?

Dalibai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumar JAMB a Najeriya ta ce babu bukatar toshe Intanet kafin a dakile satar jarabawa

Satar jarabawa ta zama ruwan dare a lungu da sako a fadin duniya kuma kasashe na daukar matakai don dakile hakan ciki har da toshe layukan sadarwa.

Hukumomi a Najeriya sun dade suna kokawa kan yadda dalibai ke satar jarabawa musamman wadanda ake yi a kasa baki daya kamar JAMB da WAEC da NECO.

Kasar Habasha wato Ethiopia ta dauki matakin katse layin Intanet da ma na sakon tes a daidai lokacin da dalibai ke kokarin fara rubuta jarrabawa a fadin kasar, wanda wasu ke hasashen cewa an yi hakan ne don a dakile satar amsa.

Katsewar Intanet a kasar ta zama jiki yayin da kasar ta shiga kwana na uku ba tare da layin Intanet ba.

A ranar Laraba gidan talabijin din kasar ETV ya ruwaito cewa an kama wasu dalibai uku da satar amsa bayan sun turawa junansu sakon tes.

Kasar Aljeriya ma ta dauki irin wannan mataki na toshe kafar Intanet yayin jarabawar kasa baki daya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kakkafa na'urorin katse layukan salula a dakin rubuta jarabawa a Aljeriya

Kamar yadda jaridar The Guardian ta Birtaniya ta ruwaito, a shekarar 2016 dalibai sama da 700,000 ne suka rubuta jarabawar fita daga sakandare wadda ake kira bac.

Ma'aikatar ilimin kasar ta soke dubbai daga cikinsu kuma ta tilasta sake rubuta wasu 500,000 ta hanyar sauya tambayoyin.

Daga bisani hukumomi sun kama mutum 31 ciki har da ma'aikatan hukumar ilimi da ake zargi da aikata laifin.

Baya ga wannan dambarwar, hukumar ilimin a shekarar 2017 ta kafa na'urorin katse layin salula a dakunan jarabawa 2,100 a fadin kasar kuma ta toshe Facebook da Twitter da Instagram.

Kasashe kamar Syria da Iraq da Mauritania da Uzbekistan duk sun bi sahu wajen toshe kafar Intanet ko kuma shafukan sada zumunta.

'Daliban ba sa karatu'

Malam Mahmud Sulaiman malami ne a makarantar sakandare ta GGISS Zaura Danbaba a jihar Kano kuma ya ce Intanet ce kawai madogarar dalibai.

Ya kara da cewa: "Daliban yanzu babu ruwansu da karanta littafi, idan jarabawa ta zo sai su shiga Intanet su karanta abubuwa su shiga dakin jarabawa.

"Akwai shafuka na musamman da aka bude wadanda aikinsu kawai shi ne su rubuta amsoshi, inda dalibai ke bayar da kudi ko katin waya kafin su samu.

"Idan aka toshe tabbas satar amsa za ta ragu, domin kuwa wajibi ne su karanta litattafansu".

Mahmud ya ce sun sha kwace wayoyin salula daga hannun dalibai a dakin jarabawar.

Ko zai yi aiki a Najeriya?

BBC ta tuntubi mai magana da yawun hukumar JAMB Fabian Benjamin, wadda take shirya jarabawar shiga jami'a da kwalejoji ga miliyoyin 'yan Najeriya.

Kuma a shekarar 2015 ne ta fara gudananr da jarabawar ta hanyar amfani da komfuta a madadin takarda da biro da aka saba, inda a wannan shekarar dalibai kusan miliyan biyu ne suka rubuta.

Benjamin ya ce babu bukatar toshe Intanet a Najeriya game da jarabawar JAMB domin ba da Intanet suke gudanar da ita ba.

"Jarabawarmu muna yin ta ne kawai a komfuta ba tare da Intanet ba sannan kuma ba ma bari dalibai su shiga dakin jarabawar da wayoyinsu na salula balle ma su yi amfani da su.

"Muna da manhaja wadda take toshe layukan Intanet a jikin komfutocinmu ta yadda ko da ka shiga da wani layin Intanet ba zai yi aiki ba.

Wasu ma'abota shafukan sada zumunta na BBC sun bayyana ra'yoyinsu.

Yayin da wasu ke ganin zai taimaka, wasu kuwa gani suke satar jarabawa ga dalibai tamkar hanta da jini ne.

Labarai masu alaka