Na mika nasarar da na samu ga Allah - Abba gida-gida
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Na mika nasarar da na samu ga Allah – Abba Gida-Gida

Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce ya mika nasarar da ya samu a Kotun Koli kan zaben fitar da gwani ga Allah madaukakin sarki.

Alkalan kotun sun tabbatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Kaduna wacce ta yi watsi da bukatar Ibrahim Al'amin (Little) na cewa PDP ba ta yi zaben fitar da gwani ba.

Kotun ta ce Little, wanda ya yi nasara a kotun farko a Kano, ba shi da hurumin shigar da kara kan zaben da bai shiga ba.

Ga abin da ya shaida wa Wakilin BBC a Kano Ibrahim Isa:

Labarai masu alaka