Amurka ta zartar da hukuncin kisa ga masu aikata fyade

Amurka
Image caption Dakin da ake aiwatar da kisan wanda hukunci ya hau kan shi

Gwamnatin Amurka ta zartar da hukuncin kisa a karon farko cikin shekaru 16.

Za a aiwatar da hukuncin kisa ga wasu mutane biyar da aka samu da laifin fyade da kisan kai, an kuma tsara kashe su a watannin Disamba da kuma Janairu.

Babban lauyan gwamnati William Barr ya ce za a aiwatar da hukuncin ga wasu karin mutane domin tabbatar da adalci ga iyalan wadanda masu laifin suka kashe.

Daraktan cibiyar samar da bayanai kan hukuncin a birnin Washington Robert Dunham ya shaidawa BBC cewa ba su yi mamaki da wannan sanarwar ba.

A cewarsa daman shugaba Donald Trump na goyon bayan yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka aikata muggan laifuka, kuma ya sha sanya tsauraran hukunci kan hakan ciki har da masu saidawa da safarar muggan kwayoyi da wadanda aka samu da aikata kisa.

To sai dai kungiyoyin da ke rajin kare hakkin dan adam sun soki wannan mataki, ciki har da Cassy Stubbs ta kungiyar American Civil Liberties inda ta ce ta damu matuka ganin yadda za a zartar da hukuncin cikin gaggawa ba tare da bada ratar lokaci ba.

Ta kara da cewa ana bukatar lokaci kafin zartar da hukuncin kisa, amma a wannan akwai gaggawa a ciki ta yadda babu tazarar azo a gani tsakanin hukuncin farko da na biyu.

A yanzu akwai mutane 62 da ke jiran hukuncin kisa da suka hada da Dzhokhar Tsarnaev da ya dasa bam a lokacin wasan tsere a Boston shekaru shida da suka wuce.

Labarai masu alaka