Burin Trump na gina katangar Mexico zai cika

Iyakasr Amurka da Mexico
Image caption Katangar da za a gina a iyakar Amurka da kudancin Mexico za ta kai tsawon mil dubu biyu

Kotun kolin Amurka ta sharewa gwamnatin shugaba Trump hanyar yin amfani da kudin ma'aikatar tsaro ta Pentagon don gina katangar da ya yi alkawarin yi tsakanin kasarsa da Mexico tun a lokacin yakin neman zabe.

A ranar juma'a ne kotun kolin ta bai wa shugaba Trump din wannan karfin iko, inda ake ganin burinsa ya cika.

Wannan katanga dai ana bukatar zunzurutun kudi har Dala biliyan biyu da miliyan dari biyar wajen gina ta.

Daman dai tun da fari 'yan majalisa daga dukkan jam'iyyun Republican da Democrat ne suka kada kuri'ar da ta hana MistaTrump samun wannan dama.

Kotun kolin ta ce wadanda suka ki amincewa da fitar da kudin ba su kawo wata hujja da za a dogara da ita ba wajen yanke hukuncin, inda batun kwararar 'yan ci-rani zuwa Amurka da sauran kasashen turai abu ne da a halin yanzu ke ci gaba da zama babbar barazana ga tsaron kasashe.

A shekarar 2017 ne dai Mista Trump ya sanya hannu kan kudurin da zai bayar da dama a fara gina kantanga a kan iyakar kasar da kudancin Mexico.

Sannan ya umarci a fara hana kudade isa ga wasu biranen Amurka da ke haba-haba da bakin haure.

A wata hira da kafar yada labarai ta ABC, Mista Trump ya ce kasar Mexico ce za ta biya ta kudin da za ta kashe wajen gina katangar.

Amma ya ce daga farko Amurka ce za ta dauki nauyin aikin gina katangar mai tsayin mil 2,000, kafin daga baya Mexico ta mayar mata da kudinta abin da Mexicon ta ce ba za ta sabu ba.

Labarai masu alaka