'Iran na tare da magoya bayan El-Zakzaky'

Hassan Rouhani
Image caption A hukumance Iran na goyon bayan 'yan gwagwarmayar addini kamar Sheikh Zakzaky

Ana ci gaba da takun saka tsakanin mabiya mazahabar Shi'a da gwamnatin Najeriya, kuma akullum batun sako malamin na daga cikin abin da ke sanya magoya bayansa yin zanga-zanga.

Ko a makon da ya wuce sai da suka gudanar da muzaharar matsawa gwamnati lamba dan ta sako jagoransu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da tun a shekarar 2015 gwamnati ke tsare da shi.

An yi bata kashi tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro da suka maida martani da hayaki mai sa hawaye da harbin dinga, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar babban jami'an 'yan sanda da wani dan jarida ya yin mabiya mazhabar Shi'a suka yi ikirarin an kashe musu mutane 20.

Kasar Iran wadda ita ma ta ke bin tafarkin mazahabar Shi'a na sanya ido kan abin da ke gudana a Najeriya kan batun, sannan abu ne da Iraniyawa suka dauka da muhimmanci.

Su na kallon gwagwarmayar da kungiyar Islamic Movement Of Nigeria ke yi a matsayin wadanda ke bin tafarkin tsarin addini guda karkashin mazahabar Shi'a, musamman a daidai wannan lokacin da rikici ke kara ta'azzara tsakanin mabiya Shi'a da Sunni a kasashen duniya.

Haka kuma, su na amfani da kafafen yada labaran Iran, dan nuna goyon baya ga kungiyar 'yan uwa musulmi. Sai kuma wani batu na daban da ake ganin ya na taka rawa wajen karfafawa kungiyar gwiwa, wato yadda 'yan siyasar Iran suka shiga ciki.

Sun taba rubuta wasika da yawancin 'yan majalisar dokokin Iran suka rattabawa hannu da aka aikewa gwamnatin Najeriya tare da bukatar ta saki Sheikh Zakzaky, ta bashi damar barin kasar ya kuma gudanar da ryuwarsa cikin 'yanci.

Sannan masu sukar lamirin shugaba Hassan Rouhani su na yawan magana a kafafen yada labarai kan ya kamata ya sanya baki a batun tare da daukar matakin gaggawa dan ganin lamura sun daidaita ga mabiya Shi'a a Nigeria.

Wasu na kallon wannan batu na kungiyar Islamic Movement of Nigeria ta fuska biyu, na farko akwai siyasa da kuma addini ne. Ta fuskar addini ana magana ne akan wani Malamin mazahar Shi'a a wata kasa da ya ke fuskantar matsin lamba, dan haka ake kira ga gwamnatin Iran ta nuna goyon baya gare shi albarkacin addini guda da suke yi.

Ta fuskar siyasa kuwa za a iya cewa Iraniya musamman masu ruwa da tsaki a gwamnati su na ganin ya yin da kasashen yammacin duniya ke sukar yadda kasar ke tsare daya daga cikin jagororin 'yan adawa, a bangare guda ba su yi wata rawar gani dan a sako Sheikh Zakzaky ba.

Dan haka su ke cewa batun kare hakkin dan adam da suke yin yekuwa kan wasu tsirarun mutane kadai ya ke fadawa musamman idan aka ce lamarin bai shafi na su ba.

Abu mai muhimmanci shi ne, a hukumance Gwamnatin Iran ta sanar da goyon baya ga duk 'yan gwagwarmayar addini kamar Sheikh Zakzaky a duk inda suke a fadin duniya.

Labarai masu alaka