Mahalarta bikin tafarnuwa sun ga takansu

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda mahalarta bikin suka rinka neman mafaka

An kashe mutum uku tare da jikkata wasu 15 bayan da wani dan bindiga ya bude wuta a wurin wani bikin bajekolin abinci a arewacin jihar California ta Amurka.

Shaidu sun ce wani mutum ya bude wuta a wurin wani bikin bajekolin abinci.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda mutane ke gudun tsira daga harin.

Wadanda suka halarci bikin sun ce an shiga rudani da hayaniya a wurin lokacin da dan bindigar ya bude wuta a dai dai lokacin da ake shirin kammala bikin na kwana uku.

Shaidu sun ce mutane sun kwanta a kasa yayin da wasu suka arce domin neman wurin tsira.

'Yan sanda sun ce jami'ansu sun tunkuri maharin nan take bayan da ya fara harbin inda suka kashe shi.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jami'an agaji sun isa wurin cikin gaggawa

Ana hasashen cewa ya shiga wurin ne bayan ya kaste wata wayar da aka sa a katangar wurin.

'Yan sanda sun kuma ce mai yiwuwa akwai wani da ke taimaka masa amma babu tabbas kan rawar da ya taka. Sun kuma kara da cewa har yanzu wurin na da hadari.

Bikin ya kunshi bajakolin abinci da kada-kade da kuma gasar girke-girke.

Bikin, wanda ke samun halattar dubban mutane, ana gudanar da shi a wani dandalin shakatawa, kuma masu shirya shi sun bayyana a shafinsu na intanet cewa ba a yarda a shiga da makami ko wanne iri ba.

Gwamnan California Gavin Newsom ya bayyana harin da cewa mummunan aiki ne.

Labarai masu alaka