Ronald Reagan ya ce 'yan Afirka birrai ne

Tsohon shugaban Amurka Ronald Raegan ke nan

Tsohon shugaban Amurka Ronald Raegan ke nan
Image caption Raegan ya yi mulki ne tsakanin 1981 zuwa 1989

A cikin wani sautin muryarsa da mujallar The Atlantic ta wallafa a shekarar 1971 lokacin da yake gwamnan jihar California, tsohon shugaban ya bayyana 'yan Afirka da ke wakiltan kasashensu a Majalisar Dinkin Duniya a matsayin birrai.

Ya furta wadannan kalaman ne na batanci a wayar tarho, a yayin hira da Richard Nixon wanda a lokacin shi ne shugaban kasar.

Labarin ya taso ne a yanzu bayan da wata kotu ta bayar da umarnin a sake duba sautukan bayan rasuwar tsohon shugaban, wanda sai yanzu ne ake da damar yin hakan bisa dalilan sirri sannan kuma a wallafa sauran bangarorin hirar.

An gano cewa Mista Nixon yana nadar dukkanin wayoyin da yake yi da Mista Reagan.

Gwamnan ya fusata ne a lokacin kan yadda masu wakiltar Afirka a Majalisar Dinkin Duniya suka ki goyon bayan Amurka wajen aiki da China, da kuma yin watsi da Taiwan.

Bayan da aka kada kuri'ar, sai mambobin masu wakiltar Tanzania suka fara rawa a zauren na Majalisar Dinkin Duniya.

Kwana daya bayan hakan, Mista Reagan ya kira Mista Nixon ya tambaye shi ko ya kalli yadda aka gudanar da kada kuri'ar a talabijin.

Sai ya ce: "Kalla yadda birran nan daga kasashen Afirka suke zaune cikin annashuwa, har yanzu ba su saba da sanya takalma ba."

Kalaman da ya sa Mista Nixon fashewa da dariya.

Mista Tim Naftali, wani farfesan tarihi a jami'ar birnin New York wanda yake kula da dakin karatun gwamnati na Nixon ne ya fitar da sautin.

Tun daga shekarar 2007 dai har 2011, shi ke kula da dukkanin sautukan Mista Nixon.

A cikin makalar da aka wallafa a The Atlantic, Naftali ya yi bayanin yadda aka cire kalaman na batanci daga hirar ta su lokacin da aka saki wani bangarensa a shekarar 2000 domin wasu dalilan sirri, a lokacin dai Mista Reagan na da rai.

Naftali ya bayyana cewa wata kotu ce ta yanke hukuncin cewa sai an kara duba sautukan:

"Mutuwar Reagan a shekarar 2004 ta dauke damuwar da ake da ita a kan sirri kuma a matsayina na mai bincike, na bukaci da a sake duba sautukan wadanda suka shafi Ronald Reagan, a cikin makonni biyu da suka gabata, sai aka saki gaba daya sautin muryoyinsu na 1971 wanda ya shafi Reagan.''

A cewar Naftali, Mista Reagan ya kira Mista Nixon domin ya matsa masa ya janye daga Majalisar Dinkin Duniya amma daga baya sai kalaman Mista Reagan kan 'yan Afirka ya zama babban abin da suka tattauna a kai.''

A cikin wata hirar da Mista Nixon ya yi da sakatariyarsa kuma sai ya kara furta wasu kalaman.

A cewarta, ga kalaman da ya furta mata, "Na ga wadannan mutanen masu akidar zamanin da. Ba su ma sa takalma ba, gashi kuma Amurka za ta rungumi aiki da su.''

Labarai masu alaka