Fafaroma Francis ya ce ba ya tsoron Cocin Katolika ta rabu

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fafaroma Francis ya ce ba ya tsoron Cocin Katolika ta rabu

A lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa Rum bayan ziyarar da ya kai Mozambique da Madagascar da kuma Mauritius, Fafaroma Francis, ya amince cewa akwai bangarori da ke da sabani da kuma sukar tsarin shugabancinsa, hatta a fadarsa ta Vatican.

Fafaroman ya ce wasu daga cikin masu sukar lamirinsa, sukan yi masa murmushi sosai amma idan ya juya ba ya sai su caka masa wuka.

Ya kara da cewa suna jifa da dutse, amma su boye hannunsu saboda ba sa so a gane su ba, sannan kuma ba sa so su ji martaninsa a kan sukar da suke yi masa.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fafaroma Francis na gaisawa da masu bi a birnin Antananarivo, Madagascar

A wani taron manema labarai na tamkar kulli-kurciya, wato a yi nan a yi can, a cikin jirgin saman Fafaroman, shugaban na darikar Katolika, a taron ya tabo batutuwa da dama, kama daga hana amfani da leda da robobi a birnin fadar Fafaroman, Vatican City,

zuwa batun kyamar baki a Afirka ta Kudu, Fafaroma Francis ya ce yana maraba da tattaunawa mai ma'ana, amma ya yi gargadin cewa akidoji na haddasa rarrabuwar kai a Cocin Katolika.

Yayi nuni da wani littafi da aka wallafa kwanan nan mai suna 'How Americans Want To Change The Pope' wato yadda Amurkawa ke son sauya Fafaroma, littafin da ke magana kan masu hamayya da shi a Amurkar.

Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY
Image caption Faraoma ya ce ba a Amurka kawai ake sukarsa ba hadda a cikin majalisar gudanarwar Cocin nasa ana yi

Ya ce matsalar rarrabuwa a addini aba ce da ta samo asali a coci tun farkon-fari a Littafin Sabon Alkawari wato New Testament.

Ya ce yana fuskantar zarge-zarge da dama wadanda ba na gaskiya ba ne, ciki har da wanda ake ce masa cewa shi dan gurguzu ne.

A kan haka ya yi gargadin cewa muddin wata akida ta shiga ka'idar addini, to ba shakka za a iya samun rarrabuwa.

Fafaroman ya ce shi ba ya tsoron rarrabuwa a Cocin, kuma yana maraba da duk wata dama ta tattaunawa da me sabanin ra'ayi da shi.