Gwamnatin Kamaru na neman sulhu da 'yan tawayen yankin Ingilishi

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A wani jawabi na masamman da ya yi ga al'umar Kamaru, Shugaban kasar Paul Biya ya ce za a kira wani babban taro domin yin muhawara da 'yan aware masu yunkurin ganin an raba kasar.

Wannan matakin na Shugaban kasa shi ne domin a ga bayan rikicin yankin renon Ingila wanda ya debi tsawon shekara 3 yana ci.

Rikicin na yankin masu amfani da harshen Ingilishi ya haifar da asarar rayukan jama'a da dama; farar hula da sojoji, tare kuma da asarar dukiya.

Gwamnatin dai ta yi ta lalube a duhu game da hanyoyin da za a samu fahimtar juna tsakaninta da 'yan tawaye na yankin da aka lakaba wa suna 'Ambazonia'.

Su dai 'yan awaren na yankin da ake amfani da harshen Ingilishi na kokarin ganin an raba kasar ce zuwa gida biyu.

Suna neman hakan bisa dalilansu na cewa gwamnatin kasar tana nuna masu wariya.

Sai dai yanzu haka wasu daga cikin al'ummar kasar ta Kamru sun fara mayar da martani kan matakin da gwamnatin ke shirin dauka.

'Duk 'yan kasar Kamaru na cikin murna da wannan jawabi da shugaban kasa ya yi, na kiran babban taro na kasa, domin neman bakin zare game da jihohin da suka butulce wa kasarmu' in ji Muhammadu Kabiru, wani mazaunin Ngaundare.

Salatu Amadu shi kuma cewa ya yi 'Mafi yawa ba mu ji abin da muke so ba, ya ce za a tattauna, to da wane ne za a tattauna? Ba mu san yanda shugaban kasa yake nufi ba.'

Amadu ya ce tabbas akwai danniya da yawa, domin bangaren masu amfani da turancin Ingilishi ba su taba samun matsayi a gwamnatin shugaban kasar ba.

Labarai masu alaka