Za a kafa gwamnatin hadin gwiwa a Sudan ta Kudu

President Salva Kiir (right) and Riek Machar (left) have been holding face-to-face talks Hakkin mallakar hoto South Sudan Government
Image caption Shugaba Salva Kiir (dama) da Riek Machar (hagu) na tattaunawa kai tsaye a Juba

Shugaba Salva Kiir da babban jagoran masu adawa da shi Riek Machar sun cimma wata yarjejeniya ta kafa gwamnatin rikon kwarya.

Ministan yada labarai na kasar ya bayyana cewa za a kafa sabuwar gwamnatin daga yanzu zuwa tsakiyar watan Nuwamba.

Shugabannin biyu na wata ganawa ta kai tsaye a birnin Juba, wanda shi ne babban birnin Sudan ta Kudu.

A bara sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta kawo karshen yakin basasan da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban 'yan kasar.

Amma gwamnatin kasar ta ce ba ta da kudaden da za ta shigar da tsofaffin 'yan tawaye cikin rundunar sojojin kasar.

Wannan na cikin matakan da aka shirya aiwatarwa domin hada kan 'yan kasar da kawo karshen yake-yaken da suka daidaita kasar tun bayan da ta sami 'yancin kai a shekarar 2011.

Labarai masu alaka