Naziru Sarkin Waka 'ya gaza cika sharuddan beli'

NAZIRU SARKIN WAKA Hakkin mallakar hoto NAZIRU SARKIN WAKA / INSTAGRAM
Image caption Naziru Sarkin Wakar Sarkin Kano

Wata kotu a jihar Kano ta tsare Naziru Ahmed Sarkin Wakar Sarkin Kano a gidan yari sakamakon rashin tantance wadanda za su tsaya masa.

Yanzu shahararren mawakin yana tsare ne a gidan yari na unguwar Goron Dutse da ke Kano.

Tun da fari dai kotun ta bayar da belinsa a ranar Alhamis bisa sharadin kawo wandada za su tsaya masa da tare da bayar da naira 500,000 da kuma kawowa kotu fasfonsa na fita kasashen ketare.

Gurfanar da fitaccen mawakin na zuwa ne bayan da rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke Najeriya ta gurfanar da shi a gaban kuliya.

Lauyan Nazir Ahmad Barista Sadik Sabo Kurawa ya shaida wa BBC cewar da zarar sun kammla matakan tantancewar zuwa gobe Juma'a za a saki wanda suke karewa.

Ana tuhumar Naziru ne kan wasu wakoki da ya yi kusan shekaru hudu da suka gabata.

Wakokin sun hada da Gidan Sarauta da Sai Hakuri.

An kama mawakin, wanda shi ne sarkin waka na Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ranar Laraba da yamma.

Ranar Alhamis ne kotun ta bayar da belinsa bisa sharadin cewa zai bayar da fasfo dinsa da kuma samar da mutanen da zasu tsaya masa.

Mutanen sun hada da dagacin unguwar da yake zaune da ma'aikatan gwamnati biyu, kuma zai biya kudi ₦500,000.

Image caption Musbahu M Ahmad da Malam Sadiku Muhammad 'yan uwan Nazir na zaman sauraren yadda shari'ar za ta kasance

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC cewa sun kama mawakin ne "saboda kalaman batanci" da ya yi a cikin wasu wakoki.

Ko da yake bai yi cikakken bayani kan kalaman da suke zargin mawakin da yi ba, ya bukaci wakilin BBC ya bi su kotu inda za a gurfanar da Naziru M. Ahmad domin samun cikakken bayani.

Sai dai Malam Aminu Saira, dan uwan mawakin, ya sanar da BBC cewa 'yan sanda sun sanar da su cewa gwamnatin jihar Kano ce ta sa aka kama shi ta hannun hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

A cewarsa, "An kama Naziru ne saboda fitar da wani kundin waka da ya yi mai suna 'Gidan Sarauta' da kuma 'Sai Hakuri'. Mun yi kokari a ba mu belinsa jiya [Laraba] da daddare amma an ki."

Image caption Yadda kotun unguwar Rijiyar Zaki ta cika da masu sauraren shari'ar

Sai dai hukumar tace fina-finai ta jihar Kano bata ce komai a kan batun ba, domin kokarin da muka yi na ji daga gare ta kawo yanzu ya ci tura.

Dan uwan nasa ya kuma ce jami'an 'yan sanda sun je gidan mawakin, kuma sun yi bincike amma babu abin da suka dauka.

Masu lura da al'amurn yau da kullum a jihar Kano na ganin akwai siyasa cikin lamarin, ganin cewa Sarkin Waka Naziru mai ra'ayin Kwankwasiya ne, wadda kungiyar siyasa ce da ke adawa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano.

Hakkin mallakar hoto Instagram/Naziru Sarkin Waka

Wasu kuma sun ce akwai wata waka da Nazirun ya rera, wadda a cikinta suka ce ya yi kalaman da suka bata sunan gwamnan Kanon.

A 'yan watannin da suka gabata, wasu mawaka har da 'yan fina-finan Hausa sun sami matsala da Kano State Censorship Board, hukumar da ke tace bidiyo da fina-finai ta jihar Kano.

Cikin wadanda aka kama a baya akwai Sadiq Zazzabi da Sanusi Oscar, wadanda a halin da ake ciki su ma suna fuskantar shari'a kan wasu tuhume-tuhume da hukumar tace fina-finan ta shigar da kara a kai.