Saudiyya ta kama malamin da ya 'soki casu'

Sheikh Omar al-Muqbil Hakkin mallakar hoto @OmarMuqbil / Facebook
Image caption Sheikh Omar al-Muqbil

A wani bidiyo, Sheikh Omar al-Muqbil ya bayyana rashin amicewarsa da yawan mawakan da masu wasannin shakatawa daga kasashen waje ke kara kwarara zuwa cikin Saudiyya daga bara zuwa yanzu.

Cikinsu akwai shahararrun mawaka kamar Janet Jackson da Mariah Carey - wadanda a baya 'yan Hizban kasar ke dode sassan jikinsu a hotuna domin kare al'ummar kasar daga gurbatar al'adu.

Sheikh al-Muqbil na ganin sauye-sauyen da ake kawowa a kasar na son wuce gona da iri, kuma ya ce suna shafe al'adun al'umomin kasar masu dadadden tarihi.

A wannan dalilin shi ma hukumomin kasar sun kama shi - kamar yadda suka kama wasu gomman malaman addini da suka soki matakan da gwamnatin kasar ke dauka wadanda ta ce za su zamanantar da kasar ne.

Amma yawancin mutane ba sa mayar da hankali kan halin da wadannan malaman ke ciki saboda ana fi mayar da hankali kan batun matan da ake tsare da su domin suna fafutukar samun 'yanci - wanda wannan alama ce da ke tabbatar da har yanzu hukumomin Saudiyya ba sa kyale duk wanda suke ganin yana son yi musu gyara ko mai kankantarsa.

Labarai masu alaka