'Yan Kannywood sun yi raddi kan kama Naziru Sarkin Waka

Naziru M. Ahmed Hakkin mallakar hoto Twitter/@Sarkinwakah
Image caption Naziru M. Ahmed shi ne sarkin wakar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kuma mabiyin akidar siyasar Kwankwasiyya ne masu adawa da gwamnatin jihar Kano

Jaruman fina-finan Kannywood da masu ruwa da tsaki a masana'antar sun soma yin martani kan kama shahararren mawakin nan na Hausa, Naziru M. Ahmad.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kama mawakin ne ranar Laraba da yammaci "saboda kalaman batanci" da ya yi a cikin wasu wakokinsa.

Ta ce ranar Alhamis za ta gurfanar da shi a gaban kuliya.

Amma Malam Aminu Saira, dan uwan mawakin, ya sanar da BBC cewa gwamnatin jihar Kano ce ta sa aka kama shi ta hannun hukumar tace fina-finai ta jihar Kano "saboda dalilai na siyasa.

Har yanzu dai gwamnatin bata ce uffan a kan wannan zargi ba.

Naziru M. Ahmed shi ne sarkin wakar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kuma mabiyin akidar siyasar Kwankwasiyya ne masu adawa da gwamnatin jihar Kano.

'Yan kannywood sun yi ta tsokaci kan lamarin a shafukan sada zumunta.

Jan kunne

Mawaka da 'yan wasan fina-finan Hausa da masu bayar da umarni sun nuna goyon bayansu ga mawakin da kuma sukar matakin kama shi inda suke amfani da maudu'in #freenazirusarkinwaka, wato a saki Naziru Sarkin Waka.

Nazifi Asnanic, wani mawaki kuma mai shirya fina-finai, ya wallafa wani hoton bidiyo a shafinsa na Instagram inda ya yi amfani da kalaman da ke nuna cewa wasu masu mulki ne ke da hannu da kama Naziru.

"Na lura an so a rika amfani da karfin iko ana rayuwa irin ta dabbobi, saboda dabbobi ne a daji idan an fi karfinka ake turmushe ka a mayar da kai abinci", a cewar Nazifi.

A bidiyon, Nazifi ya bayyana cewa duk da yana bangaren masu mulki ne, wannan matakin shi ma ya shafe shi.

"Kar ku ga cewa wai don ni ina kusa da masu abin, bai shafe ni ba. Ni ma abin ya shafe ni."

Kazalika, jarumi Nuhu Abdullahi ya wallafa wani sako a shafinsa na Instagram inda ya yi zargin cewa a siyasar Kano "ba ka isa ka bayyana siyasarka ta ra'ayin kashin kanka ba, sai a ci zarafinka."

Ya yi tambayar cewa "mawaka da 'yan fim ne kadai ke siyasa a jihar Kano da ake kama su?"

Nuhu ya kuma yi shagube cewa "Ci gaban da ka kawo guda daya ne a Kannywood, na kai 'yan Kannywood gidan yari, kuma a haka kake tunanin za ka samu goyon bayan 'yan Kannywood?"

Ita kuwa jaruma Hadiza Gabon, wacce a baya suka sha soyayya da Naziru M. Ahmed, wallafa hotonsa ta yi a Insatgram, tana mai daga hannu domin rokon Allah.

Shi ma jarumi Ali Nuhu ya yi roko ga hukumar tace fina finai ta jihar Kano "ta yi sassauci ga kaninmu kuma abokin sana'armu @sarkin_wakar_san_kano. Allah ya kawo maslaha cikin gaggawa, amin."

Mai bayar da umarni kuma jarumi, Falalu Dorayi, shi ma ya wallafa wani sako tare da hoton Naziru a shafinsa na Instagram inda ya bayyana cewa wanda ya aika wa Naziru da sharri ta hanyar tozarta shi da cin zarafinsa, ya saurari sakamakonsa.

A cewarsa "sharri mai dawowa ne komai tsayin zamanin zalunci."

Ya kuma ce akwai ranar da shugabanni masu zalunci za su gurfana a gaban Allah.

"Idan abin da Shugaba yake yana masa dadi a nan duniya, minti daya cikin kabarinsa zai gane tarin masifar da ya daukowa kansa," in ji Falalu.

Labarai masu alaka