Kim Clijsters: Za ta dawo fagen Tennis bayan yin ritaya a 2017

Kim Clijsters Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsohuwar lamba daya ta duniya a wasan Tennis Kim Clijsters za ta koma fagen daga.

Clijsters za ta ci gaba da fafatawa a fagen Tennis, inda za ta fafata a gasar WTA Tour, wadda za a gudanar a shekarar 2020.

'Yar wasan 'yar kasar Belgium mai shekara 36, wadda ta rike kambun gwarzuwar fagen Tennis ta duniya a baya, ta yi ritaya ne a shekarar 2007, domin ci gaba da kula da iyalanta.

Ta daina buga wasa ne bayan shekara biyu da lashe babbar gasar Grand Slam ta US Open.

Ta sake dawowa fagen Tennis a shekarar 2009, inda ta lashe gasar US Open da Australian Open kafin sake yin ritaya a shekarar 2012.

"A gaskiya ba zan iya tabbatar da wani abu ba. Sai dai ina ganin wannan zai kasance kalubale a gare ni, "in ji Clijsters

Lokacin da ake hira da ita a shirin WTA ta kara da cewa: har yanzu ina kaunar fagen Tennis.

Sai dai abin tambayar shi ne, shin ko zan iya kai wa matakin da nake bukata da kuma yadda zan fafata a wasan, ma'ana ko zan iya kasancewa gwarzuwar fagen Tennis ta duniya?

"Ina son na kalubalanci kaina, kuma ina son na kara jajircewa sosai. Wannan burina ne."

Clijsters na shirin dawow fagen Tennis din ne a watan Janairu, sai dai ta ce za ta ci gaba da shirye-shiryen tunkarar gasar ta badi.

A matsayinta na gwarzuwar Tennis ta daya a duniya a baya, Clijsters ta cancanta ta fafata a gasar WTA.

Sai dai tana bukatar ta fafata a wasanni uku domin samun maki 10 da zai bata damar sake rike kambunta na baya.

"Kim Clijsters ta kasance cikin gwarazan Tennis kuma komawarta fagen daga ya janyo hankulan magoya bayan ta da kuma da dama daga cikin tawagar WTA."a cewar shugaban WTA Steve Simon.

"Ina son na sanarwa magoya na cewa ina gab da komawa daga a fagen Tennis nan ba da jimawa ba," in ji Kim a shafinta na Twitter.

Clijsters ta lashe gasar WTA har sau 41 a baya, kuma ta rike gwarzuwar tennis ta duniya tsawon mako 20.

Shahararriyar 'yar wasan ta haifi 'yarta mai suna Jada a shekarar 2008, inda ta haifi 'danta na biyu mai suna Jack a 2013 sai kuma na uku wato Blake a 2016.

'Yar wasan ta ce ta dauki tsawon shekaru biyu tana wasiwasin komawa fagen na Tennis.

Labarai masu alaka