Pogba, Martial, Shaw, Dalot ba za su buga wasan Leicester ba

Pogba da Martial Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pogba da Martial ba za su buga wasan ba

Ole Gunnar Solskjaer na tsaka mai wuya yayin da Manchester United ke karbar bakuncin Leicester City a Old Trafford a yau Asabar.

Paul Pogba da Anthony Martial da Luke Shaw za su kalli wasan na karfe 3:00 agogon Najeriya daga wajen fili bisa dalilan jinya.

A gefe guda kuma babu tabbas a kan koshin lafiyar Aaron Wan-Bissaka da Jesse Lingard.

Yayin da Diogo Dalot da Eric Bailly su ma ke jinya, Solskjaer zai gamu da babban cikas musamman ganin yadda Leicester City ke wasa a kakar bana.

Har yanzu ba a ci zakarun Premier na 2015-216 ba a bana, inda suka yi canjaras biyu kuma suka ci wasa biyu.

Ita kuwa United wasa daya kawai ta ci, inda aka ci ta daya kuma ta yi canjaras a wasa biyu.

Idan har Wan-Bissaka bai buga wasan ba to babu mamaki Ashley Young ya maye gurbinsa a bangaren lamba 2, shi kuma Marcos Rojo ya buga 3.

A cikin wadanda suke a hannu, Solskjaer zai yi bakin kokarinsa wurin karfafa 'yan wasan gabansa wadanda har yanu ake ganin kansu bai daidaita ba.

Daniel James ne yakan buga bangaren hagu a gaban kuma mai yiwuwa a fara da shi a yau, yayin da Rashford zai buga 9 saboda rashin Martial.