Shugabanni kusan 20 za su halarci bikin binne Mugabe

Iyalan gidan marigayi Robert Mugabe Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Iyalan gidan marigayi Robert Mugabe

Shugabannin kaasashen Afirka na da, har da na yanzu na ta isa birnin Harare domin halartar bizne gawar marigayi Robert Mugabe.

Cikinsu akwai shugaban Equatorial Guinea - wanda ya hau karagar mulki tun kafin Robert Mugabe ya zama shugaban Zimbabwe, kuma fiye da shekaru 40 kenan babu alamar zai sauka daga mukaminsa.

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ne ya bayyana halin da ake ciki sa'o'i kadan kafin a fara shirin birne tsohon shugaban - ya ce kowa ya san Mista Mugabe mutum ne mai dumbin kuar-kurai manya da kanana.

Thabo Mbeki ya ce Amma kada mu ce komai a kan wannan batun yanzu.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan Zimbabawe na duba gawar tsohon jagoran kasar Robert Mugabe

A gefe guda kuma, da alama an shawo kan wata takardama kan inda yafi dacewa a birne tsohon shugaban Zimbabwe.

Daga baya, iyalan Mista Mugabe sun hakura - sun kuma amince a binne gawar Mista Mugaben a Heroes Acre - wata makabarta ta musamman da ake binne wadanda suka yi gwagwarmaya wajen kwato wa kasar 'yanci.

Da farko iyalan gidan marigayin sun so a gina masa wani katafaren daki ne a mahaifarsa, dakin da zai zama makwancinsa na din din din, amma aka yi ta kwan gab kwan baya har zuwa lokacin da aka shawo kansu.

A karshe dai takardamar binne Mista Mugabe ta yi kama da yadda ya gudanar da rayuwarsa a lokacin da yake raye.

Labarai masu alaka