Ukraine: Majalisar Amurka ta fara yunkurin tsige Trump daga mulki

Donald Trump Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban wani kwamiti mai karfin iko a majalisar Amurka ya ce kalaman da Shugaban kasar Donald Trump ya furta a yayin da suka tattauna ta wayar tarho da shugaban Ukraine na iya bayar da damar a tsige shugaban kasar daga mukaminsa.

Adam Schiff ne shugaban kwamitin da ke sa ido kan bayanan sirri da na tsaron Amurka, kuma yana matsawa Fadar White House ta saki cikakkun bayanan tattaunawar.

Kawo yanzu Fadar White House ta yi gum kan batun.

Mista Schiff ya kuma ce idan ta tabbata Mista Trump na kokarin tursasawa shugaban wata kasa ya ba shi bayanan sirri kan wani abokin hamayyarsa na siyasa, to babu makawa sakamakon laifin da ya aikata zai kasance tsigewa ne daga mukamin shugaban kasa.

Rahotanni daga Amurka na cewa Shugaba Donald Trump ya matsa wa Shugaban Ukraine Volodmir Zelenski ya sake gudanar da bincike kan dan Joe Biden, wanda shi ke kan gaba wajen neman zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat.

Wani rahoton ya ce Mista Trump ya bukaci haka ne a yayin wata ganawa ta wayar tarho da yayi da Mista Zelenski ciin watan Yulin bana.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tambaya ita ce: Shin Trump ya tursasa wa Ukraine kan Joe Biden da dan sa Hunter?

Tambaya ita ce: Shin Trump ya tursasa wa Ukraine kan Joe Biden da dan sa Hunter?

Dan Mister Biden din mai suna Hunter Biden ya taba yin aiki a wani kamfanin samar da makamashi a kasar Ukraine a lokacin mahaifinsa na rike da mukamin mataimakin shugaban kasa na Barack Obama.

Kuma an ce Joe Biden ya taba gargadin Ukraine yana cewa Amurka za ta janye tallafin da take ba kasar idan ba a kori wani jami'i da ke gudanar da bincike kan ayyukan da kamfanin dan nasa ke yi a kasar ba.

Amma binciken da aka gudanar daga baya ya wanke kamfanin na Hunter Biden domin an gano cewa mutumin da ke gudanar da binciken na da tabo a bangaren cin hanci da rashawa.

Mista Trump ya amince cewa ya tattauna kan batun kuma ya ambaci sunan Joe Biden a yayin tattaunawarsu, kuma ya ce yana da 'yancin yin haka.

Mista Biden ya ce Mista Trump ya aikata babban laifi - kuma ya bukaci da a gudanar da bincike kan batun.

Labarai masu alaka