'Yan tada kayar baya sun kashe daruruwan 'yan Nijar

Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Boko Haram

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe mutum 250 a hare-haren da 'yan tada kayar baya suka kai a Nijar tsakanin watan Janairu da Agustan 2019.

An kashe fiye da fararen hula 250 kuma kusan wasu 240 an sace su daga Janairu zuwa Agustan 2019, a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijar, da yankin Tillaberi da Tahoua a yammacin kasar.

Wadannan wurare ne da kungiyoyi masu tayar da kayar baya ke gudanar da ayyukansu, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a cikin wani rahotonta.

Kuma wadannan ne alkaluma mafi yawa da aka samu tun da aka fara hare-haren.

Wani rahoto da ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (OCHA) ya bayyana cewa:

"Tuni an zarce adadin yawan mutanen da aka kashe da wadanda aka sace na shekarun baya, inda aka kashe fiye da mutum 250 kuma aka sace wasu 250 din."

Rahoton ya ce a yankin Diffa, wanda ya sha hare-haren kungiyar Boko Haram tun 2015, an kai hare-hare 173, wanda suka yi sandin mutuwar mutum 202.

Kuma rahoton ya ce mata da kananan yara ne suka fi yawa, inda adadinsu ya zarce kashi 70 cikin 100 na wadanda aka sace.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A yankunan Tillaberi da Tahoua da ke kusa da iyakar Nijar da kasar Mali kuwa, an kai hare0hare 79, wanda yayi sanadin kashe mutum 42, kuma19 sun sami raunuka, ban da 15 da aka sace.

Rahoton ya ce yankin Maradi da ke kudu maso tsakiya ma bai tsira daga irin wadannan hare-haren ba.

Amma a nan ana alaknta hare-haren ne da wasu kungiyoyin masu aikata manyan laifuka daga Najeriya.

Hukumar OCHA ta ce an kai hare-hare 24 da suka yi sanadin kashe fararen hula 13, inda rahoton ya kuma ce an sace mutum 28 tsakanin watannin Janairu da Agustan bana.

Labarai masu alaka