Ko kun san abin da kasafin kudin Najeriya na 2020 ya kunsa?

  • Usman Minjibir
  • BBC Hausa

Shugaban Muhammadu Buhari ya gabatar da daftarin kasafin kudin Najeriya wanda ya wuce naira tiriliyan 10, ga zauren majalisar dokokin kasar a ranar Talata.

BBC Hausa ta zakulo muku wasu abubuwa muhimmai guda 10 da suka banbanta kasafin kudin 2020 da sauran shekarun musamman shekarar 2019 wadda aka samu rudu tun farkon gabatarwar.

1. Lokacin da Shugaba Buhari ya shiga zauren majalisar dokoki domin gabatar da kasafin kudin, zauren ya dauki sowa 'Sai Baba', sabanin a lokacin gabatar da kasafin 2019, inda wasu daga cikin 'yan majalisar suka hau yi wa Shugaban Ihu a yayin gabatar da kasafin.

Hakan dai na yin nuni da irin yadda alaka tsakanin bangaren majalisa da na zartawarwa ta kyautata sabanin yadda alakar ta kasance a majalisa ta takwas.

2. Kasafin 2020 ya kafa wani tarihi da ba a taba yin irinsa ba, inda a karon farko wani shugaban Najeriya ya gabatar da kasafin kudi da wuri. A bara dai Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin ne a ranar 19 ga watan Disamban 2018.

3. An gina kasafin kudin na 2020 ne a kan dala 57 farashin gangar danyen mai kuma bisa gangar danyen mai miliyan 1.86 da kasar za ta rinka fitarwa a kullum, sabanin dala 60 ga farashin danyen mai da ganga miliyan 2.3 a kullum da aka gina kasafin kudin 2019 a kai.

4. Kasafin 2020 ya kai naira tiriliyan 10.33, inda na shekarar 2019 ya kama naira tiriliyan 8.83, abin da ke nuni da cewa an samu karin kaso 9.7 a kan na bara.

5. A kasafin kudin bara, an ware naira tiriliyan 2.14 domin biyan basussuka, inda a kasafin 2020 aka ware naira tiriliyan 2.45 domin a biya basukan.

6. Dangane da gibin da kasafin na 2020 yake da shi kuwa, Shugaba Buhari ya ce akwai gibin nairai tiriliyan 2.18, inda kasafin 2019 yake da naira tiriliyan 1.86.

7. Shugaba Buhari ya sanar da kara haraji a kan kayayyaki daga 5% zuwa 7.5%, domin cikasa gibin kasafin na 2020.

8. A kasafin na 2020, an ware naira tiriliyan 2.46 ga manyan ayyuka, inda a 2019 aka ware naira tiriliyan 2.28 abin da ke nuna karin naira biliyan 18 a kan na bara.

9. Ma'aikatar tsaro da ta lafiya ne suka fi samun katso mai tsoka a kasafin 2019 inda suka samu naira biliyan 62 kowacce. To amma a kasafin 2020, ma'aikatar ayyuka da gidaje ce ta samu kaso mafi tsoka na naira biliyan 262.

10. Kafin fara gabatar da jawabin daftarin kasafin na 2020, Shugaba Buhari cikin raha ya sanar da zauren majalisun cewa yana fama da mura a saboda haka a gafarce shi.