Rwanda ta bude kamfanin kera wayoyin hannu na Android

A worker operates a Mara X smartphone during the launch by Rwanda's Mara Group in Kigali Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani ma'aikaci na nuna samfurin wayar Mara a wurin bikin da aka yi a Kigali

Rwanda ta bude masana'antar hada wayar salula ta farko a Kigali, babban birnin kasar.

Shugaba kasar Paul Kagame ya halarci wannan muhimmin bikin bude masana'antar da zai rika samar da wayar hannu da ake sa ran za ta rika ja dda wayoyin da ake kawo wa daga China da kasashen Asiya.

Kuma wayoyin za su rika amfani da manhajar Android Operating System ne, inda ake sa ran a rika sayar da su daga kwatankawacin dalar Amurka 190 zuwa 130.

Shugaban kamfanin na Mara Group, Ashish Thakkar ya bayyana wa kamfanin dillalncin Labarai na Reuters cewa kamfaninsa shi ne irinsa na farko a nahiyar Afirka.

Kamfanin zai rika kera dukkan kayayyakin da ake bukata domin samar da wayar salula a cikin Rwanda, ba yadda ake shigo da kayayyakin daga kasashen ketare ba.

Ana bukatar kera fiye da kayayyaki 1,000 kafin a iya hada wayar ta hannu guda daya.

Amma wayoyin hannun da ake sayarwa a kasashen Afirka sun fi na kamfanin Mara arha, kuma suna iya daukan katin SIM biyu.

Akwai kuma kamfanonin da ke hada wayoyin salula a Masar da Habasha da Aljeriya da Afirka ta Kudu, amma akan shigo da kayayyakin hada su ne daga nahiyar Asiya.

Kamfanin Mara Group ya ce ya kashe dala miliyan 24 wajen kafa masana'antar, kuma ana sa ran za a rika kera wayoyin hannu 1,200 a kowace rana.

Shugaba Paul Kagame na Rwanda na son ganin 'yan kasarsa sun kara rungumar amfani da wayoyin hannu, wanda a halin yanzu kashi 15 cikin 100 na 'yan kasar ne kawai ke amfani da wayoyin - wanda bai taka kara ya karya ba.