Kocin Super Falcon Thomas Dennerby ya ajiye aiki

Thomas Dennerby Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Thomas Dennerby ya ajiye aikin Super Falcons saboda sabaninsa da NFF

Kocin kungiyar kwallon kafa ta mata 'yan Najeriya Thomas Dennerby ya ajiye aikinsa shekara daya karewar kwangilarsa a kungiyar.

Thomas Dennerby mai shekara 60 ya kaurace wa wasanni biyun karshe da kugiyar Super Falcons ta yi, saboda takun saka tsakaninsa da hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF).

Dan kasar Sweden din ya kuma kaurace wa taron sulhun da ministan wasannin kasar, Sunday Dare ya shirya.

A takardarsa ta ajiye aiki, Dennerby ya bayyana rashin biyan albashi da saba alkawuran da aka yi masa da kuma rashin hadin kai da rashin ba shi masauki a kasar a matsayin dalilansa na ajiye aikin.

"Mista Dennerby ya aiko wa NFF takardarsa ta ajiye aiki kuma hakan bai zo mana da mamaki ba kasancewar ya kauracewa kungiyar a watan jiya," wani babban jami'in NFF ya sheda wa BBC Sport.

"Ya ce yanzu ya mika al'amarin ga lauyoyinsa kuma NFF za ta fitar ta sanarwa a kan lamarin a lokacin da ya dace."

Karkashin jagorancin Dennerby ne kugiyar Super Folcon ta kai matakin dab da na kusa da karshe a gasan cin kofin duniya ta mata a Faransa. Shi ne kuma ya jagoranci kungiyar ta ci kofin mata ta nahiyar Afirka.

Bayan tafiyarsa a wani lokaci ne aka cire kungiyar a matakin neman gurbi a gasar Olympic ta 2020, karkashin kocin riko Christopher Danjuma, lamarin da aka yi ta mamaki

An nada Dennerby kocin Super Falcons ne a watan Janairun 2018 domin maye gurbin Florence Omagbemi. Shi ne ya jagoranci kungiyar ta lashe gasar yankin Yammacin Afirka (Wafu) a watan Mayu gabanin gasar cin kofin duniya.

Shi ne kuma koci dan kasar waje na farko da ya jagoranci kungiyar ta samu gurbi a gasar cin kofin duniya sannan ya jagorance ta a gasar. Matakin da Super Falcons ta kai a gasar cin kofin duniya a Faransa shi ne mafi girma a cikin shekara 20 - baya ga matakin dab da na kusa da karshe da ta kai a 1999.

Labarai masu alaka