Euro 2020: Ingila na tsaka-mai-wuya

'Yan wasan tawagar Ingila tare da kocinta Gareth Southgate Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shakara 10 kenan Ingila ba ta yi rashoin nasara ba a wasannin cancantar shiga cin Kofin Turai

Ingila ta gamu da rashin nasara a karon farko a shekara goma a wasan neman gurbin gasar cin kofin kasashen Turai, bayan da ta sha kashi 2-1 a hannun Jamhuriyar Czech, abin da ya kawo karshen wasanta 43 ba tare da doke ta ba, ranar juma'a.

Yanzu kasar na cikin rashin tabbas na zuwa gasar ta Euro 2020, inda sai ta jira zuwa ranar Litinin idan ta doke Bulgaria sannan kuma Kosovo ba ta doke Montenegro ba, ta samu gurbi.

Tun da farko tawagar ta kociya Gareth Southgate da ta samu gurbin na gasar ta bazara mai zuwa da nasara a wasan na Prague, amma ta kasa tabuka komai, a kan 'yan Czech din wadanda sun sauya daga yadda Ingilar ta lallasa su 5-0 a Wembley a watan Maris.

A wasan na Juma'a Ingila ta fara da kyau lokacin da kyaftin dinta Harry Kane ya ci mata fanareti minti 5 da shiga fili bayan da Lukas Masopust ya yi wa Raheem Sterling keta, amma kuma abin takaici daga nan sai labari ya sauya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fanaretin da Kane ya ci ita ce bal ta bakwai da ya ci a wasannin neman zuwa gasar ta Turai

'Yan Czech sun farke kwallon lokacin da Jakub Brabec ya ci da aka dauko kwana.

Ingila ta kasa wani katabus a wasan har Zdenek Ondrasek da aka sako daga baya ya zura mata bal ta biyu a ragarta ana saura minti hudu a tashi.

A gaba dayan wasan Ingila ba ta yi wani abin a zo a gani ba, sai dai ma ta gode wa mai tsaron ragarta Jordan Pickford ya kare hare-haren Vladimir Coufal da Masopust da kuma Alex Kral.

Shi ma golan Czech ya yi kokari da ya hana Sterling da Kane yi masa ta'annati.

Wannan ne wasan farko da Ingila ta sha kashi a matakin wasannin neman tikitin zuwa gasar ta cin kofin kasashen Turai, tun bayan da ta yi rashin nasara da ci 0-1 a kasar Ukraine ranar 10 ga Oktobar 2009.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Yanzu Cristiano Ronaldo ya ci wa Portugal bal 94

Saura bal daya kacal Cristiano Ronaldo ya ci ta 700 a wasansa na kwararru na kwallon kafa, bayan da Portugal ta kusa samun tikitin gasar ta Euro 2020, inda ta doke Luxembourg 3-0.

Sakamakon sauran wasannin na neman tikiti:

Montenegro 0-0 Bulgaria

Portugal 3-0 Luxembourg

Ukraine 2-0 Lithuania

Andorra 1-0 Mildova

Iceland 0-1 France

Turkey 1-0 Albania

A sauran wasanni 8 da za a ci gaba Asabar din nan:

Georgia da Jamhuriyar Ireland

Denmark da Switzerland

Faroe Islands da Romania

Bosnia-Herzegovina da Finland

Norway da Spaniya

Malta da Sweden

Liechtenstein da Armenia

Italiya da Girka