Matar da Buhari ‘zai aura’ ta sha mamaki — Aisha Buhari

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar Aisha Buhari da BBC Hausa

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren hirar Aisha Buhari da Awwal Janyau

Bayan dogon lokaci ba ta kasar har ake jita-jitar ta yi yaji ne, mai dakin Shugaba Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta koma kasar, inda ta sauka a Abuja a cikin daren da ya gabata kuma ta tattauna da manema labarai

A tattaunawar da ta yi da manema labarai jim kadan bayan saukarta a filin jirgin sama na Abuja, Aisha Buhari ta yi watsi da jita-jitar da aka rika bazawa cewa ta yi yaji ne inda ta ce ta tafi ne domin a duba lafiyarta sannan kuma ta samu lokaci da 'ya'yanta.

A hirar, ta yi shagube ga wacce aka ce Buharin zai aura inda ta bayyana cewa ba ta musanta batun auren ba sai da ranar auren ta wuce tukuna ta musanta.

A hirar, ta shaida cewa shekara da shekaru idan yara sun yi hutu, sukan yi tafiya su shafe kimanin makonni shida, ma'ana tafiya irin wannan mai tsawo ba yau ta fara ba.

Ta bayyana cewa a wannan karon ma da suka tafi hutu, sai ta ji alamun ba ta jin dadin jikinta sosai wanda hakan ya sa ta tsaya ganin likita wanda likitan ya bata shawarar ta tsaya duba lafiyarta.

Aisha Buhari ta bayyana cewa tuni ta dade tana jawo hankalin hukumomi da ke sa ido kan sadarwa a kasar dangane da yada jita jita.

Ta bayar da misali da lokacin da Shugaba Buhari ya yi rashin lafiya a kwanakin baya inda ta ce ana ta yada hoton gawa a motar asibiti ana cewa shi ne wanda hakan ya ja aka yi ta kiranta a waya domin tambayarta gaskiyar lamarin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Isowar Aisha Buhari

A ranar Juma'a da daddare ne Aishar ta wallafa wani hotonta tare da mai dakin jakadan Najeriya a Birtaniya Mrs Modupe Oguntade, a shafinta na Instagram suna yin ban-kwana gabanin tashinta zuwa gida.

A hoton da ta wallafa, ta yi godiya ga mai dakin jakadan, wadda ta ce ta rako ta ne, domin kamo hanyar komawa gida.

Tun a watan Agusta ne dai mai dakin shugaban kasar ta bar Najeriya zuwa aikin hajji a kasar Saudiyya, wadda daga bisani rahotanni suka ce ta wuce zuwa birnin Landan na Birtaniya.

Tsawon lokacin da ta kwashe ba tare da an gan ta a bainar jama'a ko kuma wasu wuraren taruka kamar yadda ta saba ba, ya janyo muhawara a tsakanin al'ummar kasar, inda wasu rahotanni ke cewa hakan ya faru ne saboda wani sabani da ya faru tsakaninta da wasu na kusa da shugaban, sai dai BBC ba ta iya tabbatar da sahihanci wannan magana ba.

Haka nan kuma babu wata kafa a hukumance daga gwamnatin kasar da ta yi wani karin bayani game da lamarin.

A baya bayan nan dai Aisha Buharin ta tofa albarkacin bakinta kan wasu muhimman abubuwa da suka faru a kasar ta Najeriya, wadanda suka hada da Allah-wadan da ta yi da dabi'ar wasu malaman jami'a da aka bayyana a wani rahoto na BBC suna neman yin lalata da dalibansu.

Haka kuma ta yi wani tsokaci a lokacin bikin ranar tunawa da 'ya mace ta duniya, wanda duk kafin wadannan an jima ba a ji duriyarta ba, kamar yadda aka saba.