Alamomin cutar tsananin damuwa bayan haihuwa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bidiyo: Alamomin cutar tsananin damuwa bayan haihuwa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Kun san cutar tsananin damuwa bayan haihuwa? Yagana Gambo- Dauda wata kwararriya ce kan lafiyar kwakwalwa kuma ta bayyana cewa cutar tsananin damuwa bayan haihuwa na faruwa ne idan wasu sinadarai a kwakwalwar uwa suka sauya.

"Wani lokaci kuma sauye-sauyen da kan zo a lokacin haihuwa ko bayan haihuwa kan haifar wa uwa wannan cuta," in ji Yagana.

Ta ce wani lokaci, sabbin iyaye mata kan fuskanci gajiya ko saurin hushi da dai sauransu idan sun haihu kuma wannan ba abin damuwa bane.

Amma tsananin fushi da bakin ciki da tsanar rayuwa manyan alamomi ne na cewa uwa ba ta da lafiya.

Bidiyo: Fatima Othman

Labarai masu alaka