Sabon salon hana satar amsa a Indiya ya kawo rudani

ANI Hakkin mallakar hoto ANI

Wani jami'in wata makaranta a Indiya ya bayar da hakuri, bayan da wasu hotuna na wasu dalibai da suka rufe kawunansu da kwallaye yayin jarabawa ya rinka yawo a shafukan sada zumunta.

An dauki hoton ne a lokacin wata jarabawa a wata makarantar sharar fagen shiga jami'a ta Haveri da ke jihar Karnataka a Indiya.

Hotunan sun nuna daliban makarantar zaune a cikin aji da kwalaye bisa kawunansu, an huda kwalayen ta yadda za su samu iska.

An bayyana cewa an yi hakane domin hana daliban satar amsa.

Daya daga cikin malaman makaranatar ya fito ya roki gafara bayan afkuwar lamarin.

Ya ce makarantar ta yi amfani da wannan sabon tsarin ne sakamakon ta ji labarin tsarin ya yi amfani matuka a wata makarantar.

Ya kuma bayyana cewa an yi hakan ne da yardar daliban, kuma wasu daliban ma daga gidajensu suka zo da kwalayensu.

Ya ce ''ba a tilasta wa kowane dalibi da cewa dole sa ya saka kwali a kai ba, idan za ku iya gani akwai wadanda babu kwalin a kansu .''

Hakkin mallakar hoto ANI

Ya ce ''wasu sun cire kwalayen bayan mintuna 15 wasu kuma bayan mintuna 20, bayan sa'a daya mu da kanmu muka ce kowa ya cire kwalin.''

Rahotanni sun bayyana cewa jami'ai a yankin sun garzaya makarantar bayan sun samu labarin wannan sabon tsarin da makarantar ta bullo da shi.

SC Peerjade wanda jami'i ne a kasar ya bayyana wannan sabon tsarin da makarantar ta yi gwaji a matsayin ''rashin imani.''

Labarai masu alaka