An gab da kawar da cutar Polio daga doron kasa

Cutar shan inna
Bayanan hoto,

Likitoci dai sun jima suna kokarin yi wa mutane riga-kafin polio

Wata tawagar Hukumar kwararru ta ba da shaidar cewa an yi nasarar kakkabe nau'i na uku na cutar shan inna a fadin duniya.

Tabbacin kakkabe cutar shan inna nau'i na uku da aka sanar a ranar Jma'a, na zuwa ne shekara hudu bayan Hukumar Tabbatar da Kakkabe Cutar Shan inna ta Duniya ta shaida cewa duniya ta rabu da cutar shan inna nau'i na biyu tun da farko, bayan ganin da aka yi mata na karshe a kasar Indiya a 1999.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an samu rahoton karshe na bullar cutar shan inna nau'i na uku ne cikin watan Agustan 2012 a arewacin Najeriya.

Kuma tun daga lokacin ne jami'an lafiya na duniya suka tsananta ayyukan bin diddigi don tabbatar da ganin cutar ta tafi.

Samar da kwararrun ma'aikatan lafiya da dakunan bincike sun taimaka wajen fatattakar cutar daga doran kasa in ji sanarwar Hukumar Lafiya, ko da yake, ta ce sai dai kwayoyin cutar da suka rage ba su wuce wadanda aka killace a wurare masu matsanancin tsaro ba.

Ma'aikatan lafiya irin su Farfesa Abdussalam Nasidi, wani kwararre kan yaki da cutuka masu yaduwa a Nijeriya ya ce abin farin ciki ne da kuma sanin cewa makudan kudaden da aka dade ana kashewa ba su tafi haka nan ba.

Ita ma daraktar Hukumar Lafiya ta duniya reshen Afrika Dr Matshidiso Moeti, ta ce kawar da cutar shan inna nau'i na uku wani babban ci gaba ne a kokarin tabbatar da ganin an kakkabe cutar baki dayanta daga duniya.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai ta ce ba za su saurara ba, inda ta nanata cewa tilas ne kasashen duniya su karfafa gangamin alluran riga-kafi don kare al'umma, da kuma bin diddigi don tabbatar da ganin cutar ba ta sake bulla ba, sannan a samar da wani shirin kai daukin gaggawa ga wuraren da aka sake samun bayanin bullarta.

Dr Moeti ta kara da cewa wannan aiki bai kare ba, har sai an murkushe nau'i na daya daga duniya tare da damuwar bullar kwayoyin cuta da ke yaduwa daga riga-kafin da ake yi ta ce cutar shan inna guda uku ce, akwai nau'I na daya da na biyu sai kuma na uku. Dukkansu alamomin kamuwa da su iri daya ne, kuma suna haifar da nakasar da ba a warkewa, wasu lokutan abin kan zo da rasuwa.

Hukumar Lafiya dai ta ce yanzu haka kasashe goma sha biyu ne ke fuskantar bullar cutar da ake samu daga riga-kafi shan inna, kuma sun hadar da Angola da Benin da Kamaru da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da Chadi da Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo da Habasha da Ghana da Nijar da Najeriya da Togo da kuma Zambia.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce har yanzu ana samun nau'i na daya na cutar shan inna a Najeriya da Afghanistan da Pakistan, ko da yake an samu rahoton karshe na bullar cutar a Najeriya a 2016, abin da ke nufin kwayar cutar a yanzu tana bazuwa ne kadai a kasashen Afghanistan da Pakistan.