An bar matan Najeriya a baya a dukkan fannonin - MDD

Mata a yankin arewa maso gabashin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Matan da rikici ya shafa a yankin arewa maso gabashin Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan karuwar mata da 'yan mata da ake tilasta musu yin kaura da ma fasa-kwaurinsu zuwa ketare a Najeriya.

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da haka cikin wani bincike da Babbar Jami'arta kan harkokin mata, Osa Regiya, ta gudanar yayin wata ziyarar aiki a kasar.

Ta kuma koka da cewa Nijeriya ce ke da karancin mata masu rike da mukaman gwamnati a illahirin kasashen Afirka ta Yamma.

Jami'ar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ziyarci Najeriya ne domin ganin yadda ayyukan majalisar ke da tasiri ga matan kasar.

Ta bayyana wa BBC babban dalilin zuwan nata kasar: "Ina taya Najeriya murna dangane da akafa dokar hana cin zarafin mata ta shekarar 2015."

"Ina ganin wannan wani babban mataki ne aka dauka", inji ta.

Ta ce amma akwai sauran matsaloli.

"A lokacin wannan ziyara, mun lura da matsalolin da mata ke fuskanta a Najeria kamar karancin shigar mata cikin harkokin siyasa, wadanda yawansu bai kai kashi 5 cikin 100 a majalisa ba."

Ita ma ministar mata ta Najeriya, Dame Pauline Tallen ta bayyana yadda ziyarar babbar jami'a Osa Regiya za ta taimaka wa kasar.

"An bayar da karfikan taimaka wa mata da yara kanana da goyon baya, domin su ne tushen iyali."

Ministar ta ce, "Duniya fa ta sauya, kuma yanzu a ko ina cikin duniya tare da mata ake tafiya domin samun ci gaba."

Osa Regiya za ta ziyarci jihar Borno inda za ta zagaya wasu sansanonin da 'yan gudun hijira ke zaune saboda rikicin Boko Haram.