Zimbabwe za ta fitar da sabuwar takardar kudi

Zimbabwe's old currency became absolutely worthless

Asalin hoton, Reuters

Zimbabwe za ta fitar da sabuwar takardar kudi da kuma sulalla, watanni hudu bayan ta sanar da yin kwaskwarima ga takardar kudin kasar wato 'zimbabwe dollar'.

Kasar ta fuskanci karancin kudi tun a shekarar 2016, ta kuma dakatar da amfani da dalar Amurka a matsayin takardar kudin da a ke kashewa a kasar, a 'yan watannin da suka gabata a wani yunkuri na garambawul ga tattalin arzikinta.

Mafi yawan jama'a na amfani da manhajar sayen kaya ta yanar gizo, a kasar da ta yi fama da hauhawar farashin kayayyaki da karancin man fetur da wutar lantarki da kuma ruwa.

Babban bankin Zimbabawe ya sanar da fara aiki da sabuwar takardar kudin nan da mako biyu.

A shekarar 2008 ne Zimbabwe ta kafa tarihi a matsayin kasar da ta fi kowacce fuskantar hauhawar farashi mafi muni a duniya.

Yawan fitar da dalar Amurka da ake yi don biyan kayan da ake fita da su ya sa a ke samun karancin dalar a kasar.