Xhaka na tsaka mai wuya, City na neman Mikel Oyarzabal

Granit Xhaka was booed by fans as he was replaced by Bukayo Saka after his side blew a 2-0 lead against Crystal Palace

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan kallo sun rika yi wa Grant Xhaka ihu a wasan da Arsenal ta yi kunnen doki da Crystal Palace

Wasu manyan 'yan wasan Arsenal uku sun ziyarci kyaftin din kungiyar Granit Xhaka mai shekara 27 a gida bayan da ya fusata yayin wasan kungiyar Arsenal da Crystal Palace inda magoya bayan kungiyar suka rika yi masa ihu. (The Athletic).

Xhaka, dan kasar Switzerland zai gana da manyan jami'an kungiyar ta Arsenal a kwanaki masu zuwa domin tattauna matsalar da ta auku a wasan da aka buga ranar Lahadi a filin wasa na Emirates. (Sky Sports)

Ana sake alakanta kungiyar Shanghai Shenhua ta China da dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale mai shekara 30. Wannan na zuwa ne bayan da dan wasan ya kusa rattaba hannu a wata kwantiragi nan ba da jimawa ba. (Marca)

Bale ya tafi Landan domin ganawa da ajensa ranar Litinin duk da cewa akwai tababa kan ci gaba da zamansa a Bernabeu. (Mail)

Wani rahoton kuma na cewa Bale ya nemi kungiyarsa ta Real da kada ta wallafa bayanan da suka shfi koshin lafiyarsa, kamar yadda dokar Sfaniya ta ba shi irin wannan kariya. Ya dai kasa bugawa Real wasanni biyu bayan da ya sami rauni yayin wani wasa da ya buga wa kasarsa Wales. (ESPN)

Manchester City kuwa na neman Mikel Oyarzabal mai shekara 22, wanda dan wasan gaba ne na Real Sociedad da Sfaniya domin ya maye gurbin Leroy Sane na kasar Jamus wanda Bayern Munich ke nema ruwa a jallo. (sky German - a Jamusanci)

Roma ta ki amincewa da damar da aka ba ta na sayen Jack Rodwell, dan wasa mai shekara 28 wanda a baya ya taba buga wa Man City. (Corriere dello Sport - ta Italiyanci)

Ana kuma sa ran Chris Smalling, wanda dan wasan baya ne na Manchester United zai koma kungiyar bayan shekara guda da aka bayar da aronsa ta kare a Roma. Ana rade-radin dan wasan mai shekara 29 zai iya yin zamansa a kungiyar ta Italiya na din-din-din. (sky Sports)

United na son sayen wasu 'yan wasa biyu daga Faransa - Boubakary Soumare na Lille mai shekara 20, da dan wasan gaba na Lyon kuma mai shekara 23, wato Moussa Dembele. (ESPN)

Tottenham Hotspur ta sanar da Inter Milan cewa ba za su sayar da Jan Vertonghen ba a watan Janairu mai zuwa, amma kungiyar ta Italiya na fatan dan wasan mai shekara 32 zai iya komawa can bayan kwantaraginsa ta kare. (Guardian)