Mun kadu da hukuncin Kotun Koli – PDP

PDP ta ce 'yan Najeriya shaida ne kan kokarin da ta yi

Asalin hoton, The Cable

Bayanan hoto,

PDP ta ce 'yan Najeriya shaida ne kan kokarin da ta yi

Jam'iyyar PDP a Najeriya ta ce hukuncin da kotun koli ta yanke na yin watsi da karar da Atiku Abubakar ya daukaka ya ba ta mamaki.

A cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar jim kadan bayan kotu ta yanke hukunci, PDP ta ce al'ummar Najeriya ba su taba hasashen cewa haka shari'ar za ta kaya ba.

A cewar sanarwar "Ba mu kadai ba, dukkanin 'yan Najeriya har da magoya bayan APC sun ji mamakin hukuncin da kotu ta yanke".

A ranar Laraba ne Kotun Kolin Najeriya ta kori karar da jam'iyyar PDP da dan takarar shugabancin kasar jam'iyyar, Atiku Abubakar suka shigar gabanta suna kalubalantar nasarar da hukumar INEC ta bai wa shugaba Buhari a zaben 2019.

Alkalan kotun dai sun yi watsi da karar ne bisa rashin dacewarta.

Sai dai a nata bangaren, PDP ta ce ta bayar da hujjoji masu karfi wadanda ke nuna cewa Atiku Abubakar ne ya lashe zaben na watan Febrairun shekarar 2019.

Jam'iyyar ta ce a yanzu za ta dakaci hujjojin da alkalan kotun kolin suka ce za su fitar game da dalilan da suka sanya aka yi watsi da karar.