Twitter zai haramta tallan 'yan siyasa

Jack Dorsey

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mai kamfanin Twitter Jack Dorsey ya ce kamfanin zai yi cikakken bayani a cikin watan Nuwamba

Shafin sada zumunta na Twitter ya sanar da cewa zai haramta duk wani talla da ya shafi siyasa a fadin duniya.

Mai shafin na Twitter Jack Dorsey ya ce ya yin kafar internet ta ke kara karfi kuma 'yan kasuwa ke kuma amfani da ita dan yin talla a fadin duniya, hakan na yin barazana ga siyasa.

A baya bayan nan abokin takarar Twitter wato Facebook ya dauki matakin haramta tallan 'yan siyasa da abin da ya shafi siyasar baki daya.

Kafafen sada zumunta dai na fuskantar kalubale, musamman na tsaro gabannin zaben shugaban Amurka na shekarar 2020.

Haramcin dai zai fara ne daga ranar 22 ga watan Nuwamba, ya yin da za a fitar da cikaken bayanin yadda tsarin zai kasance a ranar 15 ga watan na Nuwamba 2019.

Mista Dorsey dai ya yi wannan bayani ne a wani sakon Twitter da ya wallafa a shafinsa.