Daliba ta mutu bayan dukanta a Burundi

Burundu ta haramta dukan dalibai
Bayanan hoto,

Chadia ta mutu ne sanadiyyar dukan da malaminsu ya yi mata da tsumagiya

Wata yarinya 'yar shekara 14 ta mutu bayan malamin makarantarsu ya dake da tsumagiya a birnin Bujumbura na kasar Brundi, kamar yadda mahaifinta ya shaidawa BBC.

Jean-Marie Misago shi ne mahaifin Chadia Nishime wadda malaminsu ya daketa a wuya da kafafunta da tsumagiya, lamarin da ya sanya jini ya dinga fita ta hanci da kunnenta.

''A cikin ajinsu ta mutu bayan malamin ya lakada mata dukan kawo wuka. Kuma suka ajiye gawarta a ofishin shugaban makarantar,'' inji Mista Misago.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin jami'an 'yan sanda da ma'aikatar ilimin Burundi, amma hakar ta bata cimma ruwa ba.

Mista Misago ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, kuma a wannan ranar aka binne yarinyar.

An shaida masa an daki Chadia da tsumagiya sakamakon karya wata doka a cikin aji. Hukumar makarantar ta ce ana cikin dukan wata daliba ta daban da ba ta yi aikin da aka bata ba, sai Chadia fara Farfadiya.

Dokar kasar Burundi dai ta haramta dukan dalibai da tsumagiya, ko duk wani nau'i na duka.