Mai zanen barkwanci ya harzuka Shugaban Tanzania

John Magafuli

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

John Magafuli, shugaban Tanzania

Hukumomi sun bukaci sanannen mai barkwancin nan dan kasar Tanzania Idris Sultan da ya gabatar da kansa ga 'yan sanda, bayan da ya yi shagube ga shugaba John Magufuli.

Laifin Idris Sultan shi ne hada hoton sa da na shugaban a shafinsa na Twitter, inda ya yi anfani da manhajar hada hoto ya sauya wani hoton sa da ke dauke da jikin shugaba Magufuli.

A kasan hoton wanda ya saka a shafinsa na Twitter, Mr Sultan ya yi shagube inda ya ke cewa 'mun sauya mukami ni da shugaban kasa ya-Allah ko zai samu gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarsa cikin zaman lafiya'.

A ranar Talata ne shugaban ya yi bikin cika shekaru 60 da haihuwa.

Jim kadan bayan wallafa sakon ne hukumomi su ka nemi Mr Sultan da ya mika kansa don daukar mataki na gaba.

Idan har aka ka ma shi da laifi, zai fuskanci hukunci a karkashin sabuwar dokar kasar, da ta hana cin zarafin wani mutum ta hanyar amfani da kwamfuta ko kuma shafin sada zumunta.

To sai dai masu suka na adawa da wannan doka, wadda suka ce an kirkire ta ne don hana fadar albarkacin baki.