Mourinho na son Arsenal, Ibrahimovic zai zamansa a LA Galaxy

Emile Smith Rowe, Reece James, Harvey Elliott and Brandon Williams

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon kocin Manchester United da Chelsea Jose Mourinho na son koma wa Ingila saboda yana son ci gaba da lashe manyan lambobin yabo na kwallon kafa da kungiya ta uku. (Sky Sports)

An ce Mourinho zai so ya karbi ragamar kungiyar Arsenal idan aka yi masa tayi. (ESPN)

Manchester City na son sake daukar Jadon Sancho daga Borussia Dortmund, amma dan wasan mai shekara 19 zai yi tsada matuka, inda ake hasashen zai kai fam miliyan 100. (Sport Bild, ta hannun Sport Witness)

Manajan LA Galaxy Dennis te Kloese na shirin gana wa da Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 38, domin tattaunawa kan tsawaita zamansa a kungiyar. (ESPN)

Juventus ta shirya tsaf domin sayar da Mario Mandzukic mai shekara 33 ga Manchester United ko Sevilla a watan Janairu, amma tana bukatar fam miliyan 4.6. (Calciomercato, ta hannun Mirror)

Manchester City da Arsenal na rige-rigen sayen Isco dan wasa mai shekara 27, wanda dan wasan tsakiya na Real Madrid ne da kasar Sifaniya (Mundo Deportivo, via Manchester Evening News)

Dani Alves ya ce tilas Neymar - wanda dan wasan gaba na Paris St-Germain da Brazil ne - ya sauya halayyarsa idan yana son abokan wasansa su mutunta shi, kuma ya ce a yanzu yana da halin kananan yara ne. (Spor TV, ta hannun jaridar Independent)

Joao Pedro dan Brazil mai shekara 18 ya sami izinin yin aiki a Ingila, matakin da zai ba shi zarafin buga wasa da kungiyar Watford a watan Janairu mai zuwa. An sayo shi daga Fluminense ne kan fam miliyan 2 a watan Oktobar 2018, amma tun lokacin yake dakon takardun da za su ba shi damar yin aiki a Ingila. (Standard)

Liverpool da Borussia Dortmund da kuma Barcelona na son sayen Ferran Torres, dan wasan Sifaniya mai shekara 19 daga Valencia. (Sport Bild, via Metro)