Habasha: Mutum 78 sun mutu a rikicin kabilanci

Supporters of Jawar Mohammed staged protests last week

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Magoya bayan Jawar Mohammed sun yi zanga-zanga a makon jiya

Mutane 78 sun hallaka a Habasha, kuma da alama rikicin na da nasaba da gwajin karfin iko tsakanin wani dan siyasa da firai ministan kasar.

Mai magana da yawun shugaban Habasha Abiy Ahmed ta sanar da kashe mutane akalla 78, a wani rikici da ya balle a wasu sassan kasar a makon da ya gabata.

Jami'an tsaro sun sanar da kama sama da mutum 400 da su ke zargi da hannu a aiwatar da kashe kashen da kuma lalata dukiyoyi.

Rikicin ya barke ne bayan da wani mai karfin fada a ji a kabilar Oromo, Jawar Mohammed, ya sanar a shafinsa na Facebook cewa gwamnati na barazana ga rayuwarsa.

Kalaman na jagoran na zuwa ne bayan da gwamnatin ta janye jami'an tsaron da ke ba shi kariya.

To amma tuni gwamnatin shugaba Abiy Ahmed ta musanta wannan zargi.

A cewar mai magana da yawun shugaban, Ms Billene, rikicin na da nasaba da kabilanci da kuma bambancin addini.

'Yan sanda a yankin na Oromia da tashin hankalin ya fi shafa sun ce mutane 68 ne a ka kashe.

A watan da ya gabata ne a ka karrama Mr Abiy da lambar girmamawa ta zaman lafiya da ake kira 'Nobel Peace Prize'.

An ba shi lambar yabon ce a kan rawar da ya taka wurin kawo karshen rikici tsakanin kasarsa da Eritrea mai makwabtaka, da kuma yunkurin daidaita al'amura a Habasha.