Ashe tsohon shugaban Kenya Moi bai mutu ba?

Daniel Arap Moi
Bayanan hoto,

An yi ta yada labarin mutuwar tsohon shugaban Arap Moi a shafukan sada zumunta na internet

Mai magana da yawun tsohgon shugaban Kenya Daniel Arap Moi, ya ce labarin da aka yi ta yadawa na mutuwar shugaban na kanzon kurege ne.

Mr Lee Njiru ya ce labarin da akai ta yadawa a shafukan sada zumunta na internet ba su da tushe bare makama.

Tsohon shugaban mai shekara 95 ya dade ya na fama da rashin lafiya, inda ya ke yawan kwanciya a asibiti.

Mr Lee ya ce idan labarin mutuwar Arap Moi gaskiya ne, ba bu wanda zai boyewa al'umar kasar Kenya.

Shugaban shi ne na biyu da ya jagoranci kasar bayan karbar 'yancin kai, ya kuma gaji mulkin daga hannun marigayi Jimo Kenyatta mahaifin shugaba mai ci Uhuru Kenyatta.

Ya kuma yi mulkin Kenya na tsahon shekara 24, tun daga shekarar 1978 zuwa shekarar 2001