'Tsofaffin ma'aikatan Twitter na yi wa Saudiyya leken asiri'

Twitter Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ana tuhumar wasu ma'aikata biyu na kamfanin fasaha na Twitter da laifin yi wa kasar Saudiyya leken asiri.

Ali Alzabarah da Ahmad Abouammo tare da Ahmed Almutairi wanda ma'aikaci ne a fadar gidan sarautar Saudiyya na fuskantar tuhuma saboda yi wa wasu masu amfani da shafukan Twitter kutse.

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta ce tana tuhumar mutanen biyu da yi wa kasar Saudiyya aiki ne ba tare da sun yi rijista da hukumomin kasar ba.

Ma'aikatar shari'ar ta bayyana cewa mutanen biyu sun taba amfani da damar da suke da ita ta kasancewa su ma'aikatan kamfanin Twitter ne, inda suka yi kutse cikin sakonnin email da wayar wani sanannen mai sukar gwamnatin Saudiyya.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar shari'ar ya kuma ce mutanen na iya amfani da bayanan da suka sato daga shafukan sada zumunta na mutumin domin gano wasu masu amfani da dandalin na Twitter da suke da alaka da mutumin.

Ya kara da cewa Amurka ba za ta kyale wasu mutane su yi amfani da kamfanonin kasar da fasahar da Amurka ta mallaka domin cin zarafin jama'a ba.

Kawo yanzu Saudiyya ba ta ce uffan ba kan wannan batun, amma masana sun ce ba su yi mamakin matakin da Amurka ta dauka ba, musamman saboda irin rawar da Saudiyya ta taka wajen kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi a bara.

Labarai masu alaka